Film dinda yafi kowane kawo kudi tun lokacin da aka Fara film din Hausa (Kannywood)

Jarumin na Kannywood wanda har ila yau yana shirya fina-finai sannan yana rera waka, ya ce “na fara harkokin fim ne a Kano inda nake share-share da goge-goge a masana’antar kade-kade da ake kira ‘Landscope Studio’.”
Game da abin da ya sa ya shiga harkar fina-finai, Adam ya ce, “tsoron kada na zama dan jagaliyar siyasa ko kuma dan shaye-shaye ne ya sa na tsunduma harkar.”
Adam, wanda ake yi wa lakabi da ‘Usher’ wata inkiya da ta samo asali tun yana makarantar sakandare saboda iya rawa, ya fito a fina-finai fiye da 100, a inda kuma ya shirya wasu fiye da 20.
A fagen waka kuwa, jarumin yana da kundi guda shida kuma kowane kundi na dauke da wakoki 12, a inda wakarsa mai taken Gumbar Dutse ta zama bakandamiyarsa.
Adamu kamar yadda har ila yau wasu suke kiransa, ya ce a duk fina-finansa, ya fi son Ahlil Kitab saboda irin gudunmawar da ya bai wa addinin Musulunci a cikinsa, kamar yadda ya bayyana.
Sai dai kuma fim din da ya yi mai taken Gwaska shine fim dinda yafi kowanne kawo kudi a masana’antar kannywood, duk da cewa shi ma fim din ya ci fiye da naira miliyan bakwai kafin a kammala shi.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15