Adadin kudinda neymar ke kar6a a PSG


Neymar bai buga wa Paris St-Germain gasar cin kofin Faransa wato Ligue 1 a karawar da ta tashi babu ci da Montpellier a ranar Asabar, sakamakon jinya da yake yi. Dan wasan ya koma PSG da taka-leda kan fam miliyan 200 daga Barcelona a matsayin wanda aka saya mafi tsada a duniya a fagen tamaula. Sai dai ana rade-radin cewar dan wasan na tawagar Brazil yana karbar fam 88,552 a kowacce rana, kimanin fam miliyan 2,718,126 a duk wata. Mujallar Der Spiegel ce ta fitar da wannan rahoton inda ta kara da cewar Neymay yana karbar fam 3,542 a duk sa a daya kamar yadda Marca ta wallafa. Wata mujallar Paris match ta ce an girke jami'an tsaro da suke kula da lafiyar Neymar a katafaren gidansa da ke kilomita 14 tsakaninsa da wurin atisayen PSG.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.