Rahama Sadau ta Maida Martani ga Yaran Ali Nuhu


Masana'antar fim an santa da abin kunya. Duk abinda dan wasa zaiyi bazai tsira daga idon Jama'a ba kuma kuskure karami idan suka aikata zai iya zama babba. Wani lokaci za'a iya cewa abin kunya akwai amfani da yawa kamar yadda akwai rashin amfani ga dan wasa. Saboda wannan dalili, wasu daga cikin waÉ—annan 'yan wasan kwaikwayon sunayin abin da ganganci don yada sunansu ga jama'a yayin da wasu suka yi ba tare da suna so ba. Babu wanda ya yi rikici a Kannywood fiye da Rahama Sadau kwanakin nan. A ranar Asabar ne kuma ta sake shiga wani inda yaran Ali Nuhu suka zazzagawa yar wasan kwaikwayon Zagin kare dangi a kan shafin yanar gizo na Instagram suna zarginta da cin amana ga Ali Nuhu duk da cewa shi ne shugabanta kuma ya kasance tare da ita duk rintsi duk wuya. Jita-jita ta yadu cewa Rahama basa dadi da Ali Nuhu saboda bai saka ta a fim din da FKD zasu shirya ba mai suna Abota. Da aka tamabayi Rahama Sadau dan jin ta bakinta, sai tace " wannan jita-jita ne marar tushe balle makama wanda aka yada dan kawai a bata mata suna. Nayi mamaki da cewa akwai wadanda zasu yadda da wannan maganar " "ko kuma kunyi imani da wadannan jita-jita? " ta tambayi yan Jarida. Sannan ta kara da cewa " Babu wani abu da ya hada ni da Ali Nuhu. Yaya ma wannan zai yiwu? Ahh! " Ta kara da cewa itama taga zagin da ake mata ne bayan wani abokin aiki ya kirata kuma ya gaya mata ta shiga Instagram domin taga abin da ke gudana. Ta bayyana cewa mutanen da suke zaginta suna bakin ciki da Nasarar da kuma ci gabanta ne. Har yanzu muna iya tunawa da cewa Rahama Sadau bata dawo kannywood ba a hukumance a wanda hakan ya jefa ayar tambaya ga mutanen da suke jifanta da zagi, duba da Girman Ali Nuhu a kannywood yaza ace ya fara saka ta a fim alhali an haramta mata shiga, haka zai kawo kunya da rashin girmamawa ga mahukunta.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Nafi Jin Dadin Sauraron Wakar Sauran Mawaka fiye Da Tawa - Inji Nura M Inuwa

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa