Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Aminu Shariff (momo)



Daga Sa'idu Bahaushe Kodayake ban sani ba ko ka taba yin karatun aikin Jarida ko kuma yin aiki a wata kafar yada labarai ba kafin zuwanka tashar Talabijin ta Arewa24 kana gabatar da Shirin Kudin Kannywood.Amma katobar tambaya don neman suna da cewa ka kware da sakin baki ya hambarar da kai ga yin tambaya game da Addinin Allah a wajen da ba muhallinsa ba tunda shirin nishadi ne a cikin kayanka na sanyi ga Jaruma Umma Shehu. Wauta da rashin sanin makamar kwadagonka sun sanya ka yin shirme ga Addinin da ba ka isa ka bata ba ko ita Umma ta bata ba.Na daya Addinni ya kyamaci kure don tozarci,kamar yadda ya shimfida ka'idar kare mutuncin Musulmi(Momoh a duba Arba'unan Nawwawi)!Ina fada maka ne don ka mai da maganar nishadi ta Addini alhali babu kira bai kamata mu ga gawayi ba,ballantana abin da ya ci shi! Ga wasu 'Yan tambayoyi don Allah.Ko meye burgewa idan ka bayyanawa Musulmai da wadanda ba Musulmai ba cewa wani Musulmi bai fahimci komai a cikin Addininsa ba? Ko a tunaninka gyara ne don gaba ko kure ne da tozarci ka yi? Ko a matsayin ka na Dan Fim nasara ce idan ka wulakanta Abokiyar Sana'arka da ta fiddo ka tare da yi maka Riga da Wando? A matsayin na Babban mai gabatar wa ko me ka jawo wa wurin aikinku da irin wannan shibircin aikin da bai kai ko da darajar ruwan Aski ba?

KARANTA:- Yadda momo ya kunyata umma shehu a wata hira da sukayi

A ganinka yadda kake hira da su da irin wannan salon kana dariya,nan gaba da bayyanar haka wasu za su ci gaba da halartar shirin naka,to ci gaba ko aikin mai ginin rijiya? Da a ce kokarinka na mai kwazo ne a harkar Addini da bakinka bai sanya ka bar shirin ya fita ba tunda za a Iya tace shi! An ta jin Hujjojin buge na cewa ita ta tado maganar to kai aikin me kake yi a matsayin(anchor) watau Madugun gabatarwa?Kai sai ka zama rakumi marar akala bayan ka yi takalarka! Zai kyautu hukumomin tashar su taka maka birkin karfe don ka San me za ka rika fada lura da sukar da tashar ke Sha kan bata tarbiyya daga wadanda ke caccaka! Bai kamaci mai hankali ya Yanke mata hukunci da cin mutuncinka ba lura da ba-zata,kamar kuma yadda ya kamata kowa ya fahimci cewa ka nufi daji. Amma tunda da Addini ka ke, to kazo da wuta maishi nada ruwa.! Mun dauko daga shafin instagram na @kannywoodexclusive

Comments

  1. Enter your comment...kai wayace ma duk dan jarida abinda ya keyi.Kashi 40 na 'yanjarida ba shi ne profession dinsu ba,korewarka wajen magana da nazari ke baka daman takawa.
    MOMO yayi daidai don 'yan jarida na tambaya fiye da haka

    ReplyDelete
  2. Gaskiya wa kake da suna ma way saidu ba haushi ko. Da alamar akwai wauta akwakwalwarka. kuma kafita daqiqi in har kaga hhirara da kyau kake wannan shirmen. Wanan Yar fim din dakake Karewan, Ita ta janyo tambayan da kanta. tunda itata fara cemai bata kallon fim sai sauraron waka. da ya tambayi dalili tace ai bata da lokacine saboda tana tafiya makaranta daga safe har yammaci. ya tambaya yaji wani irin makarantane tace Islamiya. Kuma Kar kamanta wannan Shiri ne kan Rayuwa jarumi, duk inda ake irin wannan shira Ko turawne kawai tambayarka ake yi sake kan rayuwanka, daga tambayar da akaima za aiya ciro wata taambaya. don haka shi Momo bai da wani laifi. ita da tayi karya dai ta ga karshen karya kenan hadi da daqiqan ci. Ai ba a iya cutan yanayi. kaikuma kaje kasa kedubawa da idon basira kasa hankalinka sosai. baka ganeba kanimi wani yama bayani. bakazo karinka ma mutane rashin kunyaba.

    ReplyDelete

Post a Comment

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.