Karuwan kan samu gidaje a unguwanni masu tsada inda sukan kama haya su biyu ko uku a a ɗaki, kuma sun samu ƙwarewa ta musamman na yaudarar manyan masu kuɗi a wuri tatrurrukan aure kona “Birthday” da ire-iren su domin samun masu neman hulda da su.
LEADERSHIP A Yau ta gano cewa ɗaukar irin waɗannan matan na tsawon dare yana kamawa ne daga N30,000 zuwa N50,000 hakan ya kuma danganci wuri da waɗanda suka haɗa “Harkar” matan ne kan zaɓi wurin da za a yi “harkar” saboda dalilan tsaro in an cimma inda za a haɗu, matan kan zaɓi zuwa wurin “Haɗuwar ne a motar hawansu ko kuma a wasu motocin haya masu tsada wanda akasari suna da mambobin wayar direbobin, hakan, in ji Bella wata daga cikin waɗannan mata, yakan “ƙara maki daraja wajen abokin hurɗa yana kuma nuna cewa, kin fi ƙarfin ɗan ƙaramin kuɗi” “a kwai buƙatar kashe kuɗi waje kula da jikinki da gashinki kuma dole ki rinƙa sa kaya masu tsada in har kina son mazaje masu “tsada” su kula ki, ga kuma kuɗaɗen haya da sauran na harkokin yau da kullum shi ya sa kake gani matan na neman manyan kuɗaɗe in ba haka wata rana za a bar ki a baya” in ji ta. Bayan haɗu wa da “Kwastoma” ta hannun kawalai da kuma kai tsaye a wuraren haɗuwa na kulub-kulub, waɗannan matan sun kuma ƙware waje tallata kan su a hanyoyin sanarwa na zamani irin su Instagram da Snapchat da Facebook da Tinder da kuma irinsu Instachat sukan manna hotunansu tsirara tsirara domin yaudarar mazaje su nemi huɗa da su.
“ni ba na neman mazaje a kulub a Instagram nake haɗa harka na bayan mun daidaita da juna” in ji wata karuwar bayan da wakilinmu ya nemi ya yi huɗa da ita, ta bar shi tsaye, ta nufi wata babba mota ƙirar “Marsandi”, “amma fa ka sani ina da tsada domin na san hanyoyin gamsar da namiji” in ji ta. Jaridar LEADERSHIP A Yau ta kuma gano cewa, karuwai masu amfani da hanyoyin sadarwa na zamani kan chaji N50,000 zuwa N100,000 a dare ɗaya, ya wancin waɗannan matan kan yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen kasuwanci a ƙasashen duniya irinsu Dubai, sukan kuma yi amfani da irin wannan tafiye tafiye samun wasu “ƙwastamomin masu romo” ta hanyar ayaudara mazaje da jikinsu da kuma kaya masu tsada das u ke sawa, hanƙoronsu a koda yaushe shi ne yadda za su tabbtar da akwai wani “ƙwastamomin masu romo” a komarsu. Amma a ɓangaren cikin garin Legas labarin daban ya ke a waje karuwan domin ko rabin takwarorinsu da ke harka a wurare irinsu ƁI da Ikoyi da Lekki da kuma Ajah a abin da ya shafi “Kwastoma” da kuma tsarin rayuwa da irin kuɗaɗen da su ke caza, haka kuma a kwai bambanci a irin wuraren da suke aikata masha’ar.
Misali a wurare irin su Ikeja da Maryland da Yaba da Surulere da Ojodu da kuma Ogudu wuraren da matsayin rayuwa ke matsakaici kuɗaɗen da karuwai kan caja ya yi ƙasa sosai akan abin da takwarorinsu na Ɓictoria Island, kasancewa da karuwa a waɗannan unguwanni da tsawon dare kan buƙaci N5,000 zuwa N10,000 hakan ma ya danganta ne da wuri da kuma yanayin da aka haɗu. Yawancin waɗannan matan zaka samu ba su da motoci da gidaje na kansu da za su kai “kwatamominsu” sukan dogara ne a kan shi “mutumin ya ɗauke su zuwa inda za su yi harkar, su kuma masu neman na “sha yanzu magani yanzu” ya kan kama daga N1,500 zuwa N2,500. “Da yawa a cikinmu ke ɗaukar ɗawainiyar gidajenmu, saboda haka ne mu kan hurɗa da mutum dai dai gwargwadon aljihunsa” in ji Joy, wadda ke harkar karuwancinta a unguwannin Yaba da Mushin a yayin da take zantawa da wakilinmu. “ a kwai lokuttan da babu kwastoma, to dole ki yarda da mutum ko da nawa ya maki da shi, wasu lokuttan kuma in kasuwa ta buɗe har N7,000 mu kan karɓa a kwanan gida” in ji ta.
Joy, kamar yawancin mata a nan ɓangaren sun shafe fiye da shekara 5 suna karuwanci amma babu wani abin a zo a gani da suka ƙulla, ba kamar takwarorinsu na na yankin Ɓictoria Island ba wayenda suke gudanar da babbar harka, kuma basu fuskantar wata tsangwamar ‘yansanda da ‘yan iska kamar yadda ake yawan kai samame a waccan ɓangaren.
“In ba ki yi saa ba ‘yan sanda ko ‘yan iska sukan kwace ɗan abin da ki ka samu, yawancinmu mun fi shekara 5 muna karuwanci amma babu wani abin kirki da muka tara, ba don muna ɗan samun na cin abinci ba da ɗan abin da muke tura wa wa iyayenmu da ire-irena mun bar wannan sana’ar” yarinyar ta ƙara bayyanawa.
Banda rayuwa a kan titi da sauran bambance-bambance da ke tsakanin karuwan Ɓictoria Island dana cikin garin Legas, su na unguwanni kamar Lekki da Ikoyi da Ajah kan haɗu da mazaje ne ta hanyoyin sadarwa na zamani amma a kan kuma biya su kuɗaɗen harkarsu ne ta hanyar biya kai tsaye zuwa asusun ajiyarsu ta bankinsu, su kosu ko na cikin gari sukan bayyanar da tsiraicinsu ne Kai tsaye a wuraren shan barasa da ka tituna in da yawancin mazajen da ke halartar wuraren na neman mata ne masu arha kuma yawancin na wuraren ne ‘yan iska da ɓarayi ke shawagi abin da kan sa karuwan kan rasa kayayyakinsu kamar wayar salula a wasu lokutta ma ‘yan iskan kan lakaɗa masu kasha bayan yin lalata da su, irin waɗannan matan kan faɗa hannun miyagu matsafa, bayani ya nuna cewa karuwai da yawa ne suka mutu ta wannan hanyar. Jima’I da wani abun ne da Allah Ya halasta ma ma’aurata, amma yanzu ya zama wani abin da zaka gani a lowanne lungu na ƙasar nan, mata na tallarsa maza na saya, an ƙiyasta cewa miliyoyin nairori a ke samu a harkar karuwanci a duk faɗin ƙasar a kowanne shekara, wannan bunƙasar ne ya haɓɓaka ƙaruwar gidaje otal-otal da gidajen masha’a a Legas da manyan garuruwa a lungunar ƙasar nan, duk da cewa karuwanci haram a dokokin ƙasar nan amma harkar na matuƙan bunƙasa saboda tsnanin rashin aikin yi da ake fama da shi da “alherin” da ke fitowa daga wannan mummunan sana’a.
Comments
Post a Comment