Yadda wani mai gadin da ya yi lalata da yara mata 54



- An kama wani mai gadi akan zargin aikata lalata da yara yan firamare 54 - Mummunan al’amarin ya afku ne a kasar Afrika ta kudu - Ya dauki tsawon wasu lokuta yana aikata ta’asar - Mai laifin zai gurfana a gaban kotu dake Soweto Rahotanni sun kawo cewa hukumomi a kasar Afrika ta Kudu sun tsare wani mai gadi akan zargi da ake masa na yin lalata da yara 'yan firamare mata su 54. A ranar Litinin ne dai aka fara gudanar da bincike akan al’amarin, bayan wasu dalibai mata biyu sun shigar da kara, kuma tuni gwamnati ta tura jami'ai zuwa makarantar da ke Soweto a kudancin Johannesburg.
Yara mata biyu masu shekaru 8 da kuma masu shekaru 12 ne suka je ofishin 'yan sanda a ranar Litinin inda suka kai kara cewa wani mai gadi ya yi lalata da su a wata makarantar firamare da ke Soweto. Tun lokacin da aka soma bincike, sai aka gano cewar mutumin ma ya yi lalata da dalibai mata 52. Kuma ya shafe tsawon watannin 18 yana tafka mummunan aika-aikan. A ranar Laraba ne ake sa ran mai gadin zai bayyana gaban wata kotun Majistre a Soweto.
A halin yanzu kuma sashen ilimi na yankin ya tura jami'ai domin taimakawa 'yan yaran da aka ci zarafinsu sannan kuma a fadada bincike. Afrika ta Kudu ta kasance daya daga cikin kasashe da aka fi aikata fyade da kuma cin zarafin mata a duniya.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.