Karanta -Da gaske ne kungiyar Izala ta karbi 'kudin makamai'?



Daya daga cikin jagororin Kungiyar Jama'atu Izalatul Bid'ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS), Sheikh Kabiru Gombe, ya musanta zargin da ake wa kungiyar kan karbar "kudin makamai".
Ana zargin gwamnatin tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan da raba wa jama'a da kungiyoyi da kuma kamfanoni a kasar makudan kudin da aka ware don sayo wadansu makamai. Malamin ya bayyana hakan ne lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Landan ranar Alhamis tare da rakiyar Sheikh Abdullahi Bala Lau, wanda shi ne shugaban kungiyar JIBWIS.
Za ku iya kallon cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Sheikh Bala Lau da kuma Kabir Gombe idan kuka latsa nan.
"Ba mu da alaka ta kusa ko ta nesa da maganar karbar kudin makamai. Wannan abu ne da kungiyar Izala ba ta taba shiga cikin shi ba," in ji Sheikh Kabiru Gombe.
Gwamnatin Najeriya tana ci gaba da tsare tsohon mai bai wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro, Kanar Sambo Dasuki ne bisa zargin yana da hannu a badakalar kudin sayo makamai da suka kai dala biliyan biyu.
Daga shafin BBC Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15