Kun taba ganin fim din Hausa da ba soyayya?



An fara nuna wani fim din Hausa a gidajen kallo, mai fadakarwa kan fataucin mutane maimakon mayar da hankali kan soyayya kamar yadda aka saba.
Fim din dai mai suna 'Safara' an yi shi ne kan yadda ake safara da bautar da yara domin samun kudi ba tare da son ransu ba. An dauki fim din ne a jihohin Legas da Kaduna da kuma Kano.
Da yake yi wa wakilin BBC Ibrahin Isa bayani game da fim din, wanda ya shirya fim din, Isah A. Isah, ya ce fim din ya lashe naira miliyan 5.2.
Jaruman fim din sun hada da Jamila Nagudu da Ali Nuhu da Aminu Sharif Momoh da Ladidi Fage da kuma Isah A Isah.
Ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don jin karin bayanin da wanda ya shirya fim din ya yiwa BBC:
Masu fim dai suna son su cigaba da nuna fim din a sinima har sai karshen watan Nuwamba a lokacin da suke sa ran fara kai fim din kasuwa domin su samu riba.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15