Wanda ya busa usur aka gano kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m sai dai naira miliyan N860m



Mutumin da busa usur din sa yasa hukumar EFCC ta gano kudaden da aka boye a Ikoyi ya ce bai zai ansa kasa da kashi biyar ba a matsayyin la'ada
- Busa usur din mutum yasa aka gano naira biliyan N13bn a cikin wani gida a Ikoyi
- Gwamnatin tarraya ta yi alkwarin biya duk wanda ya busa usur aka gano kudadden gwamnati da aka sace kashi 5% daga cikin kudin Wanda ya busa usur din da yasa aka gano wasu makudan kudaden da aka boye a Ikoyi yaki karban Naira miliyan N325m a matsayin la’ada, sai dai naira miliyan N860m Mutumin wanda busa usur din sa yasa hukumar EFCC ta gano kudaden da aka boye a wani gida dake unguwar Ikoyi a jihar Legas yayi ikirarin cewa ba zai ansa kasa da kashi 5% ba daga cikin kudaden da aka gano ba.
Busar usur din da mutumin yayi, ya taimakawa hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gano dala milyan $43m, wanda yayi daidai da naira biliyan N13bn a kudin Najeriya daga wata gida a ikoyi.
Mutumin da ya busa usur din Ikoyi yayi ikrarin cewa ba zai anshi naira miliyan 325m, sai dai miliyan 860m kamar yadda aka mi shi alkawari.
Mai ba wa fadar shugaban kasa shawara a fannin cin hanci da rashawa ferfesa Bolaji Owasanoye, ya ce idan kudaden da aka gano suna da yawa kashin yana raguwa amma idan kudaden basu da yawa sosai kashin da za a ba wanda ya busa usur din zai karu, wannan shine aihin tsarin da ake bi a duniya.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15