Raba Kan Jama'a : Za A Maka Shugabannin Bangarorin Izala Kotu
* Mawallafin mujallar nan ta ' Desert Herald', Malam Tukur Mamu ya ba bangarorin kungiyar Izala na karkashin Jagorancin, Sheik Bala Lau da Sheik Sani Yahaya Jingir wa'adin makonnin biyu su dunkule wuri guda ko kuma ya maka su kotu.
A cikin wata doguwar makala da Mawallafin ya rubuta ya zargi shugabannin Izala da kara janyo rabuwar a kai tsakanin mabiya Sunna sakamakon son abin duniya da shugabanci wanda kuma hakan ya saba koyarwa wadanda suka assasa kungiyar, Marigayi Sheik Abubakar Gumi da Marigayi Sheik Isma'ila Idris.
Mawallafin ya ci gaba da cewa, ziyarar da Sheik Bala Lau Da Kabiru Gombe suka kai a nahiyar Turai a kwanan da sunan da'awa ya nuna cewa shugabannin sun fara wuce gona- da- iri kan yadda suke amfani da kudaden kungiyar wajen biyan bukatunsu wanda a cewarsa, an fi matukar bukatar da'awarsu a cikin gida a maimakon Turai.
Mawallafin ya nuna takaicinsa kan yadda Shugabannjn bangarorin Izalar suka mayar da kungiyar wata hanya ta samun kudade da Alfarma don biyan bukatunsu da na kusa da su, ya kuma bijora yadda shugabannin kungiyar ke bin 'yan siyasa da attajirai wanda a cewarsa, duk wadannan halaye sun ci karo da koyarwa shugabannin da suka kafa kungiyar.
Comments
Post a Comment