An haramta hawa mota a wasu yankunan Borno



An haramta zirga-zirgar ababen hawa na fararen hula a kan titunan da suka ratsa wasu garuruwa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na wani dan lokaci.
A wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar mai sa hannun kwamishinan harkokin cikin gida da watsa labarai da al'adu Mohammed Bulama, ta ce an dauki matakin ne saboda tsaron lafiyar mutane da dukiyoyinsu a jihar, bisa shawarar da Kwamandan Rundunar Lafiya Dole mai yaki da Boko Haram ya bayar.
Titunan da aka sanya wa haramcin yin zirga-zirga a kansu sun hada da wadanda suka ratsa daga garin Konduga zuwa Bama da Banki da Gwoza har Maiduguri daga Moloi, sannan zuwa Dambuwa da Gwoza.
Haramcin ya rafa aiki ne a ranar Litinin 30 ga watan Janairu, kuma zai ci gaba har zuwa ranar Lahadi 4 ga watan Fabrairu.
Gwamnatin jihar ta bai wa al'ummomin yankin hakuri a kan duk wani matsi da hakan zai jawo musu, ta kuma ce kula da tsaron al'umma da kokarin dawo da zaman lafiya yankin su ne manyan burikanta.
Sanarwar ta kara da cewa, sakamakon ci gaba da matsawa kungiyar Boko Haram lamba da sojojin kasar ke yi, ya sa mayakan na neman tsira ko ta halin ka-ka, tare da kokarin yin badda kama suna shiga yankunan fararen hula.
A don haka ne gwamnatin ta bukaci jama'a da su kara sa ido sosai wajen lura da abubuwan da ke faruwa a kewayensu, tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yar da da shi ba ga hukumomin da suka dace.
Jihar Borno dai ta shafe kusan shekara tara tana fama da rikicin kungiyar Boko Haram, wanda ya yi sanadin mutuwar dubban mutane, tare da raba miliyoyi da muhallansu.
Sai dai a baya-bayan nan rundunar sojin kasar ta ce tana dakile karfin kungiyar ta yadda a yanzu ba sa iya kai manyan hare-hare da manyan makamai, sai dai harin kunar bakin wake.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15