Ja da baya ga rago ba tsoro ba ne — Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya ce matakin da ya dauka na janye ziyarar da ya shirya zuwa Kano ba don yana tsoron wani ba ne. Ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da manema labarai a Abuja.
"Abin da ya sa na janye, saboda shugabanni a nan Abuja da Kano masu daraja, da kuma ina ganin darajar al'ummar da su ka zabemu, ba na son inje wani a ji mar ciwo, ko a ci masa mutunci, ko a wulakanta shi."
Da aka tambaye shi ko ya ji tsoron matakin da jami'an tsaro suka dauka ne, sai ya ce, "To ni da nayi ministan tsaro ma. Sojan Najeriya ma na sama na kasa da na ruwa, sunana 'Sir' fa a gurinsu."
Ya kuma kara da cewa "Ina ganin rashin zuwana a cikin wannan tsarin ya fi alheri, shi ya sa muka saurara. Kuma ina so ka sani, ja da baya ga rago bai zam tsoro ba." "Wata rana mai zuwa zan je Kano, kuma taron da za a yi zai nunnunka wannan. Kuma ba yadda wasu za su yi don hana ziyarar faruka", inji Sanata Kwankwaso.
Tun da farko dai Sanata Kwankwason ya shirya zuwa Kano ranar Talata 30 ga watan Janairu. Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce ya dauki wannan matakin ne saboda kauce wa rikicin siyasa da ka iya biyo bayan ziyarar tasa, kamar yadda Alhaji Rabi`u Sulaiman Bichi, mai magana da yawun bangaren kwankwasiyya ya shaida wa BBC.
Dan siyasar ya ce ya samu shawarwari daga bangarori da dama kan ya janye ziyarar. Latsa hoton don kallon kalaman Alh Rabi'u Sulaiman Bichi mai magana da yawun Kwankwasiyya a Kano.
A ranar Jumma'a ne rundunar 'yan sandan jihar Kano ta shawarci tsohon gwamnan da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kaiwa jihar a ranar Talata 30 ga watan Janairu, saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.
Akwai sabani mai tsanani tsakanin tsohon gwamnan da gwamna mai ci Abullahi Ganduje wadanda a da su kayi tafiya daya a siyasance.
Gwamna Ganduje da Sanata Kwankwaso sun ziyarci fadar shugaban kasa da safiyar yau Litinin, inda Kwankwaso ya gana da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, shi kuma Ganduje ya gana da shugaban ma'aikata Abba Kyari. Sai dai ba a san ko dalilin da ya kai su fadar shugaban kasar yana da dangantaka da batun sulhu tsakanin 'yan siyasar biyu ba.
Comments
Post a Comment