Jaruman Bollywood Sun Kwance Wa Firaministan Isra'ila Zani A Kasuwa

Jaruman Masana'antar fina-finai ta Indiya Bollywood Amir Khan, Salman Khan da Shah Rukh Khan sun ki amince wa da gana wa da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a lokacin da ya ziyarci kasar ta Indiya.
Firaministan Indiya narendra Modi ne ya tarbi Netanyahu a New Delhi babban birnin kasar wanda ya yi alkawarin sake karfafa alakar ısra'ila da kasar.
A yayin ziyarar ta Netanyahu an shirya masa taron cin abinci da taurarin Bollywood.
An samu labarin cewa, jarumai Amir Khan, Salman Khan da Shah Rukh Khan sun ce, sun ki msa gayyatar da Netanyahu don yin zanga-zanga ga zaluncin da ake yi wa Falasdinawatare da nuna goyon bayansu da al'umar falasdin.
Mutane da dama a shafuka sada zumunta na yanar gizo sun nuna goyon baya ga matakin da jaruman suka dauka.
Comments
Post a Comment