Kamfanin Dangote Ya Kaddamar Da Sabon Buhun Fulawa A Kano



Kwanakin baya ne manya da kananan diloli tare da shugabannin kungiyoyin masu biredi da gurasa da sauran masu sarrafa fulawar da kanfanin Dangote ke samarwa, suka halarci wani taro da kamfanin ya shirya musu a Kano, domin kaddamar musu da sabon buhun fulawa mai cin kilo 52 maimakon kilo 50.
An gudanar da taron ne a Otal din Royal Tropicana, inda ya samu halartar maza da mata. Da yake gabatar da jawabinsa ga mahalarta taron, shugaban kamfanin Hamir dake kwanar Singa Kano, wanda har ila yau daya ne daga cikin babban dilan kamfanin Fulawa da Dangoten Alhaji Hamisu Rabi’u, ya nuna matukar farin cikinsa da shirya wannan taro musamman domin kaddamar musu da sabon buhun fulawa a jihar Kano.
Shugaban na Hamir ya kara da cewa za su ci gaba da tallata wannan sabon sanfurin Fulawar, da sauran kayayyakin da Alhaji Aliko Dangote ke sarrafawa kasancewar shi dan asalin jihar Kano ne. Sannan ya ce, zai ci gaba da bayar da shawarwarin da suka kamata domin kara ci gaban kamfanin.
Alhaji Hamisu Rabi’u ya ce, daga lokacin da ‘yar Aliko Dangote watau Hajiya Halima Dangote ta fara jagorantar kamfanin na Fulawa dake Kano, aan samu ci gaba kwarai dagaske, ya ce, ta kan zauna da su domin jin matsalolinsu da kuma yadda za a kawo ci gaba a kamfanin, saboda haka manya da kananan dilolin kamfanin za su ci gaba da tallafawa domin kara bunkasa tattalin arzikin jihar Kano da kasa baki daya.
Shi kuwa shugaban kungiyar masu sana’ar Biredi na jihar Kano, Alhaji Mu’azu Ibrahim shugaban kanfanin Gidauniyar Braed, shi ma ya nuna farin ciki sosai da sabon buhun na Fulawa da kamfanin Dangote ya samar musu.
Alhaji Mu’azu ya kara da cewa, babu shakka kamfanin Dangote na matukar basu kulawar da ya dace domin bunkasa sana’arsu a jihar Kano. Shugaban na Gidauniya Bread ya yi kira ga masu wannan sana’a a jihar Kano dasu rika amfani da Fulawar Dangote, sannan kuma su sanya tsoron Allah da kwatanta gaskiya a duk lokacin da suke mu’amala da abokan ciniki, da fatan Allah ya sakawa kamfanin na Dangote da alhairi.
Shugabar kungiyar mata masu sana’ar Gurasa ta jihar Kano, Hajiya A’isha, ta kokawa ne game da yadda kamfanin na Dangote ke fifita kungiyar masu Biredi, amma yake barin kungiyar su a baya duk da kasancewar suna amfani da da Fulawar ta Dangote domin yin gurasa, duk da haka ta yi matukar murna da wannan Fulawa da kamfanin ya samar masu ta kuma ce a matsayin ta na shugabar mata za ta tabbatar da cewa duk mai wannan sana’a a jihar Kano ta yi amfani da wannan sabon buhun fulawar.
A nasa jawabin, jami’i mai kula abokan bangaren fulawa a kanfanin Dangote Malam Garba El-Suleiman ya ce, kamfanin Dangote kullum tunaninsa shi ne ya taimakawa manya da kananan masu hurda da shi musamman na can kasa.
Garba El- Suleiman ya shaidawa mahalarta taron cewa, a wannan shekara kamfanin zai taimakawa kungiyar masu Biredi da sauran masu sarrfa Fulawa na jihar Kano, tare da rarraba masu kwantainoni domin dai suji dadin gudanar da sana’arsu a duk inda suke a kananan hukumomin 44 na jihar.
Sannan kuma har ila yau kamfanin zai shirya wani babban taro a Kano domin bayar da kyaututtuka ga manya da kana nan dilolin da suke amfani da Fulawar Dangote yayin da wasu kuma za’a kai su kasar Dubai domin bude ido.
Nura Rabi’u Abdullahi manajan shiya na kamfanin Fulawar ta Dangote, ya nuna farin cikinsa sosai game da yadda ‘yankasuwar suka samu damar halartar taron kamfanin da fatan nan gaba idan aka shirya irin wannan taron zasu halarta.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15