Miliyoyin bindigogi sun shigo Najeriya ta barauniyar hanya a 2017



- An gano adadin bindigogin da su ka shigo Najeriya a sace
- Najeriya ta zama matattarar shigowar makamai a Afrika
- Ana fama da matsalar tsaro a bangarori da dama na Kasar
Wani bincike da aka yi ya nuna yawan makaman da ke barkowa cikin Najeriya y ahaura miliyan 20. Miliyoyin bindigogi su ka shigo Najeriya ta barauniyar hanya a karshen shekarar bara ta 2017.
Bindigogin da aka yi kokarin shigowa da su Najeriya kwanaki
Jaridar Sunday Tribune tace an gano makamai har 21, 548, 608 da su ka shigo Najeriya a 2017. Wannan lissafin dai bai hada da makaman da Jami’an ‘Yan Sanda su ka karbe a hannun tsageru da miyagu a cikin kasar a barar.
Jami’an fasa kauri na kwastam sun saba damke makamai da aka yi kokarin shigowa da su cikin iyakokin kasar. Ko a Legas kwanaki an yi kokarin shigo da bindigogi 440 cikin kasar a sace ta filin jirgin Murtala Muhammad.
Tun a shekarun baya dai Majalisar Dinkin Duniya tace mafi yawan makaman da ke yawo a Yammacin Afrika a Najeriya su ke karewa. Najeriya dai na fama da kalubalen tsaro a Yankin Arewa maso gabas da wasu wuraren.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15