Sheikh Abdullahi Bala Lau Ya Zama Shugaban Ahlus Sunnah Na Europe Baki-daya
Shugaban kungiyar Izalar Naijeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya zama Shugaban Ahlus Sunnah na Europe baki-daya, bayan karba gayyatar kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai.
Haka Zalika kungiyar Sautus Sunnah Europe ta gina wa kungiyar Izala Ofishi, a Cibiyar Ahlus Sunnah ta Turai baki-daya.
"Mun yi nazarin kungiyoyi-kungiyoyi na Musulunci da Ahlus Sunnah a duniya, sama da kungiyoyi sittin (60), a kasashe daban-daban.
Amma ba mu ga kungiyar da Allah Ya ba nasara cikin takaitaccen lokaci irin wadda Ya ba kungiyar Izala ba". — Inji Jagororin Kungiyar Sautus Sunnah Europe ta kasar Turai. Allah Ka kara wa kungiyar Izala albarka da daukaka. Ameen.
Daga shafin Rariya
Comments
Post a Comment