Yadda Farfesa Abdalla Ya Mayar Da ’Yan Fim ‘Mutane’
Farfesa Abdalla Uba Adamu fitaccen malamin jami’a ne, sannan mashahurin manazarci mai bincike kan adabin Hausa a tarayyar Nijeriya, Afrika da ma duniya bakixaya, kuma shi ne shugaban Buxaxxiyar Jami’ar Nijeriya, wato NOUN. Bugu da kari, a na kyautata tsamman Farfesa Abdalla ne farfesa na farko mafi karancin shekaru a Arewacin Nijeriya lokacin da ya samu takardar shaidar zama cikakken farfesan, wato shehin malamin jami’a.
To, amma duk da wannan matsayi da ya ke da shi, ya shiga tsundum cikin ’yan fim xin Hausa kuma ya wahalta mu su tare da bayar da bayar gudunmawa mai tarin yawa wajen bunkusar masana’antar, inda a kwanan nan ya gayyaci masu sana’ar da yawa ya naxa su jakadun jami’ar tasa, wanda hakan ke nuna cewa, dangantar Farfesa Abdalla da masu sana’ar shirin fim ce ta taka rawa wajen yiwuwa ko samwar hakan, domin dai kafin ya zama shugaban jami’ar ba a taba ganin hakan a baya ba.
A baya ba a taba samun wata hukuma ko ma’aikata ko kamfani ko kungiya da ta kwashi ’yan fim da yawa haka lokaci guda a matsayin jakadunta ba irin yadda jami’ar NOUN ta yi a kwanan baya ba.
Tarihi da bincike sun nuna cewa, a ko’ina a duniya a na nuna wa masu sana’ar shirin fim kyama ne a garuruwansu kafin daga bisani tilas da yanayi su saka a rumgume su.
Hakan ne ya faru ga babbar masana’antar shirin fim ta duniya, wato Hollywood, wacce ke da sharkwata a Amurka. Bincike ya nuna cewa, a farkon kafuwar masana’antar ta fara ne a birnin New York, to amma saboda irin tsangwamar da masu sana’ar ke fuskanta tilas su ka yi kaura daga birnin zuwa inda yanzu masana’antar ta Hollywood ta ke.
Ita ma masana’antar shirin fim ta Bollywood da ke kasar Indiya ta fuskanci irin wannan tsangwamar daga mutanen garuruwansu; lamarin da ya sanya yawancinsu yin kaura daga garurwansu zuwa babban birnin kasar a wancan lokaci, wato Bombay.
Yadda waxancan masana’antun shirin fim na Hollywood da Bollywwod su ka sha fama da nuna kyama a kasashensu, haka ita ma masana’antar shirin fim xin Hausa, Kannywood, ta na matukar fuskantar irin wannan tsangwama daga birnin Kano, wato garin da ta kafu ko a ce ta samo asali kuma sharkwatarta a halin yanzu.
Tarihi ba zai taba mantawa da zamanin tsohon shugaban hukumar tace finafinai ta jihar Kano, Malam Rabo, ba, wanda a lokacinsa a kai masu sana’ar ta shirin fim da dama gidan yari, sannan a ka tilastawa wasu yin gudun hijira daga jihar.
Ta yiwu wasu su xauka cewa, sai da Abdalla ya zama shugaban NOUN ne ya fara mayar da ’yan fim mutane. Ko kusa ba haka ba ne; ya janyo wa masana’antar ta Kannywood cigaba mai tarin yawa tun a can baya.
Tun shekarun farko na 2000 ya jagoranci shirya taron duniya na finafinan Hausa a Kano, wanda wannan taro shi ne irin na farko a tarihin finafinai a Nijeriya bakixaya; Kudu da Arewa. Kafin gudanar da wannan taro, a kasashen duniya da dama ba a san da masana’antar shirin fim ta Hausa ba, wato Kannywood. To, amma sai ga shi ta shallake masana’antar shirin fim ta Kudu, wato Nollywood, ta riga ta shirya wani taro wanda ya shafi duniya bakixaya a karon farko a tarihin kasar, inda masana da manazarta da sassan duniya su ka samu halarta, saboda tasirin Farfesa Adamu.
Za a iya cewa, an tallata Kannywood ta hanyar wannan taron ne, wasu daga cikin jaruman Kannywood da kamfanoni su ka fara samun ayyuka da kwangiloli daga waje, inda a yanzu wasu su na iya fita kasashen waje a dalilin sana’ar ko dai don gudanar da wani aiki ko kuma don halartar bikin karramawa, wato ‘award’.
Bugu da kari, Farfesa Abdalla ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da wanzuwar wani shirin horarwa da kyankyasar sababbin matasan marubuta a Kannywood wanda British Council Kano ta shirya a karkashin ScriptNet mai taken ‘Reel Dialogue Project’.
Za a iya cewa, wannan shiri ya samu gagarmar nasara a Kannywood, domin ya fitar da fitattun marubutan masana’antar irinsu Nasir S. Gwangwazo, wanda a yanzu shi ne shugaban kungiyar marubuta ta Kannywood, Guild of Script Writers kuma marubucin fitattun finafinai da dama da su ka yi nasara kamar Sarmadan, Waraka, Sanafahana, Kambun So, Garinm Da Nisa, Jamila Da Jamilu, Toron Giwa, Mutallab, Sabon Sangaya, Maryam Diyana, Walijam da sauransu.
Gwangwazo shi ne ya fara amfani da ‘software’ xin Final Draft a Kannywood, wacce a ke rubutun fim da ita, amma Farfesa Abdalla ne ya ba shi ita kyauta tun a wancan shekarun. Gwangwazo ya lashe ‘award’ da dama ta ‘Best Script Writer’.
Shi ma Ibrahim B. Lawan ya na daga cikin marubutan da a ka kyanykashe a shirin na Reel Dialogue. B. Lawan dai na xaya daga cikin marubutan fitaccen shirin gidan talabijin mai suna Daxin Kowa, wanda a ke nunawa a gidan talabijin ta Arewa 24 duk mako. Shirin Daxin Kowa ya zama gwarzon fim xin talabijin na ‘AMBC Award’ a 2016. Duk waxannan na daga cikin irin nasarorin da farfesan ke da hannu wajen kawo su.
A ’yan shekarun baya-bayan nan kuma Farfesa Uba Adamu na xaya daga cikin manyan mutanen da su ka yiwa wasu mambobin kungiyar ’yan fim garanto a wajen Bankin Masana’antu (Bank of Industry) a ka ba su bashin miliyoyon Naira, don su bunkasa sana’ar tasu.
Za a iya cewa, nasarorin da Abdalla ya kawo wa Kannywood su na da matukar yawa. Ma’ana; ba su kaxai kenan ba kuma hatta waxanda su ke a zahiri rabinsu ba zai faxu a ’yan waxannan shafukan ba.
Idan da sukuni, za mu cigaba, domin yabawa ma godiya ce!
Comments
Post a Comment