Rahotanni sun bayyana cewa an gano wani irin gidan karuwai amma na dabbobi wanda mutane da dama daga kasashen waje kamar su Jamus, da Holland, da Sweden da kasar Birtaniyya ke barin kasashen su don su zo kasar Serbia su biya kudi don su yi lalata da dabbobi kamar su karnuka, shanaye, akuyoyi, aladu da kuma jakuna.
An samu labarin cewa a babban birnin kasar Serbia akwai wani wurin da aka killace don gudunar da sana’ar kwaruwancin dabbobi ga mutanen da ke sha’awar jima’i da dabbobi.
Mutum zai iya shiga jirgin sama zuwa wannan kasar da ke gabashin nahiyar Turai daga birnin London ba tare da bata lokaci ba, amma wata kungiyar da ke kare hakkin dabbobi ta bayyana cewa mafi yawancin mutanen da ke ziyartar kasar don wannan mummunan abu su kan shiga kasar ta ‘bas din shakatawa’ ne.
Binciken da tashar talabijin na RTL ta gudunar game da lamarin da gano cewa akwai wani shafin yanar gizo da ke talata wannan sana’ar na jima’i da dabbobi.
Mutane na biyan kusan kudin Euros €70 zuwa €150 (wanda yayi daidai da pan £60 zuwa £135) idan aka mayar da kudin zuwa kudin Nijeriya zai kai kimanin naira N28,495.37 zuwa N64,114.57 sannan idan bakin suna so su dauka bidiyo a yayin da suke lalata da dabbobi sai sun kara biyan kudi Euros €50 a kai (wanda yayi daidai da pan £45) wato karin kusan naira N21,371.52.
A rahoton an nuna hoton wata karya ta saka wandon mata wanda ake kira da fish-net da kuma takalma masu tsini..
Shugaban wata kungiyar kare hakkin dabbobi, Pavle Bihal, ya bukaci rufe wannan gidan karuwancin dabbobin.
“Muna da masaniyya game da gidan karuwancin dabbobin, wanda daki ne a gidan haya, a ciki ne ake duk wannan abun. Mu na so mu tabbatar da unguwar da gidan ya ke kafin mu kai kara zuwa wurin ‘yan sanda.” Inji Bihal.
Makiyayan da suke gudunar da wannan sana’ar ba su ga wani matsala da ke tattare da yin hakan ba, a cewar Leviathan.
Comments
Post a Comment