Ma’auarata: Yadda Za Ki Gamsar Da Mijinki




Rubutuna na daya gabata, yana daya daga cikin rubutun danayi na samu matukar kira, sakonnin tex dana emel da yawan gaske, akasarin basu buguwa da kuma masu turo sakonnin nasu kalilan ne cikinsu da suka kushe rubutun, duk kuwa da an samu wasu da suke ganin kamar na zake a rubutun ganin na fito da wasu bayanan da ya kamata a boyesu a fili, wanda ni kuma nake ganin irin wadannan ma’auratan kodai irin mazan nan ne da basu iya gamsar da matansu ko kuma matan da basu iya gamsar da mazajensu suke neman fakewa da addini domin kushe rubutun, sai dai kuma albishir da zan musu shine abunda suka karanta kashi uku ne kacal daga cikin abunda ke dauke a cikin littafi na, domin ganin wannan mujallar yara da manya suna karantawa, yasa na sakaya wasu bayanai da suka kamata na fito dasu a fili da fatan masu karatun da suke ganin batsa tayi yawa a rubutun dasuyi hakuri su dauki darasi da illimin dake ciki su watsar da abunda suke ganin batsan ne domin su taimakawa zamantakewarsu na aure ni kuma na samu lada.

Ganin a baya munyi maganane akan yadda maza zasu gamsar da matansu na aure, wannan yasa maza da dama da suka turo sakonsu suke neman suma a illimantar da matan hanyoyin da zasu gamsar dasu suma, duk kuwa da
cewa daman ya zama dole a yi wannan rubutun domin tabbatar da dukkannin jinsunan biyu suna da illimin da zasu gamsar da juna domin gudun kada guda cutar da guda saboda rashin sani.

Gamsar da namiji a jima’ince yafi sauki wajen gamsar da mace, duk kuwa da cewa dukkannin halittan da aka yiwa mace a jima’ince suma maza suna da irinsa. Kamar yadda ake samun harijin namiji haka nan ma ake samu harijan mace, yadda ake samu mazan da suke jimawa babu gajiya a lokacin jima’i hakama matan. Ana samun maza da mata ragwaye a wajen jima’i da kuma wadanda sam jima’in ma bata damesu ba a dukkannin jinsunan biyu.


Da akwai wasu mazan da basu cika son doguwar wasannin motsa sha’awa ba, wasu kuwa suna bukatan lokaci maitsawo ana masu wasa duk kuwa da macen tafi namiji bukatar wasan motsa sha’awa mai tsawo.


Abu na farko daya kamata mace ta fahimta a tattare da mijinta shine abunda yafi bukata a yayi wasannin motsa sha’awa da kuma lokacin kwanciya irin na jima’i, domin da akwai inda da zaran mace ta tabawa mijinta maimako ta motsa mishi sha’awarsa sai kawai sha’awar tashi ya gushe. Hakama a kwanciyar jima’i, yana da kyau ki fahimci irin yanayin kwanciyar da mijinki yake so. Shi yasa malamai na jima’i sukecewa sadarwa a jima’i yanada matukar alfanu ga ma’aurata domin ta hanyarce zasu iya fihimtar abubuwan da suke bukata a yi musu kamin, lokaci da kuma bayan jima’i.



Da akwai mazan da zaran mace ta fara wasa dasu nan da nan suke gamsuwa ba tareda sun shegetaba, da akwai wadanda da zaran azzakarinsu ya shiga shikenen kuma sunyi zuwan kai kenan. A akwai mazan da sukan dauki lokacin mai tsawo suna jima’i da mace kamin suyi zuwan kai, wasu mazan kuwa a lokacin da suke kawowa a lokacin ne gabansu ke kara yin karfi har sai sun kawo sama da biyu koma biyar kamin suke gamsuwa da mace. Ke naki mijin yaya yake, domin dole sai kin fahimci yadda yake kamin ki iya gamsar dashi.


Sai dai maza masu wuyan sha’ani a jerin mazan da na ambata sune masu saurin zuwan kai da kuma masu daukan lokaci mai tsawo suna gurza mace basu gamsu ba, sai dai kuma da zaran mace ta samun illimin sarrafa irin wadannan maza ta gama dasu. Maza masu saurin zuwan kai sune mazan da sukafi cutar da matansu, domin wata matan sai ta gurzu take gamsuwa, don haka matsalar irrin wannan mazan yana tattare ne da kodai suna da cuta da suke bukatar ganin likita, ko kuma sabbin shiga ne wato mazan da suka yi aure sabo-sabo ko suka jima basu yi jima’i ba hakan na faruwa da su.


Domin samun cikenken illimin yadda zaki gamsar da mijinki, kina iya tuntubata ta email ko lambar wata domin taimaka miki da wasu shawarwari. Ganin a wannan shafin hakan bazai samu ba kamar yadda ya kamata.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15