Daga Sani Tahir Kano Ga duk mai bibiyar masan’antar shirya fina-finan Hausa wato (Kannywood), ya kwana da sanin tirka-tirkar da ta ki ci ta ki cinyewa a game da shugabannin kungiyar MOPPAN da fitacciyar jaruma Rahama Sadau, tun kusan bara aka kore ta daga masana’antar, saboda laifin fitowa bidiyon wata waka wadda ta sabada al’adar malam Bahaushe da addinishi. Korar ko dakatarwa da ta janyo rabuwar kan wasu mutane da dama, wadansu suna ganin a yi mata afuwa, wadansu kuma suna ganin kada a yi mata afuwa. Saboda a ganinsu ta karya doka. Ana cikin haka aka ji ta a wata kafar sadrwa tana mai nuna nadama da abin da tayi, inda ta neme gafarar gwamnan jihar Kano (Dr. Abdullahi Umar Ganduje da mai martaba sarkin Kano Mal. Muhammad Sunusi da al’ummar Kano da sauran ’yan Arewa. A nan fa wadanda suka dage a kan sai ta rubuta takardar neman yafiya daga kungiya ta yi, kuma kwatsam tafiya ta kama ta zuwa tallar jirgin sama, bayan ta dawo ne su kuma kungiyar masu shiryawa wato (KAPAN). Suke ganin laifin shugaban hukuamr tace fina-finai da dabi’a Fahallahu bisa fadar cewa, zai ci gaba da duba fina-finai da jarumar ta futo inda suke ganin bai dace ba. Ko ma dai mene ne ya kamata a duba ke nan Rahama sadau. Dalili kuwa shi ne duk wanda ya yi laifi har ya fitoya nuna nadamar laifin da ya yi, ya kamata ai mai afuwa, don na san duk kusan nasarar da ta samu a rayuwarta dalilin harkar fim ce. Ya kamata ita ma Rahama ta sake rubuta wa kwaminitin ladabtarwa, don durkusuwa wada ba gajiyawa ba ne. Na san mutane da dama suna yi wa kwamitin kallon kwamitin adalci. Wasu kuma suna ganin ai ko kadan ba za su yi adalci ba, suma ya kamata kungyar (KAPAN) dalilinsu duniya ta san Rahama Sadau har ake ba ta aiki, saboda irin kokarin da takeyi. Ayuba Muhammad Danzaki a ra’ayinshi kuma a matsayinshi na marubucin fim, yana ganin bai dace a kore ta ba “Da an jawo ta jiki sai a yi mata nasiha ba wai a kore ta ba. Dalili kuwa in har an kore ta sai ta je ta yi abin da ya fi wannan, in ji shi.
Comments
Post a Comment