Jerin sababbin fim din Hausa a 2017-2018


Sababbin wasannin Hausa na ci gaba da samun krbuwa. Wannan ya sa kamfanin shirya fina-finan Hausa kara samun kudi da suke shirya wasanni masu inganci sosai. Masana’antar na da masoya da dama, jarumai da kuma daraktoci masu fasaha. Sababbin fim a 2017 1. Kanwar Dubarudu A cikin wannan fim akwai manyan jarumai kamar Rahama Sadau da Ali Nuhu. Rahama da Ali Nhu sun hau matakin yaya da kanwa wanda zasu iya sadaukar da komai ga junansu. 2. Auren Manga Wannan wasa ne da ba’a gajiya da kallo. Wani jarumi Suleiman Yahaya Bosho ya kasance tauraron wannan fim inda ya hau matakin jami’in dan sanda. Falalu Dorayi ne ya yi daraktaan wannan fim mai tarin barkwanci. 3. Mansoor Umar Shareef ne ya zamo tauraron wanan fim. Ya fada tarkon soyayya, amma abubuwaa da dama sun faru da wannan labara na soyayya. Ali Nuhu, Garzali Miko, Baballe Hayatu sun kasance a fim din. 4. Rariya Rahama Sadau ta shirya wannan fim mai tarin takwa, ado da kuma rawa na zamani. 5. Mijin Yarinya Tauraron wannan wasa ya kasance wani tsoho da yake shawarar auran yarinya karama. 1. Aljannar Duniya Ya hada jarumai irin su Fati K.K Usman, Yakubu Muhammad. Labarin wani mutumi ne da yayi kokarin taimako, amma sai abun ya juye a kanshi. 2. Dare Daya Akwai jarumai kamar su Sha'Aibu Lawan, Rabiu Rikadawa a ciki. Labarin wasu ma’aurata ne da suka fuskanci kalubale da iyalansu amma sun shawo kan komai. 3. Kalamu Wahid Akwai jarumai irin su, Sadiq Ahmad, Ali Nuhu, Lawan Ahmad, Samira Abubakar. Labarin wani mutumi ne day a ziyarci abokinsa daga nan sai labara ya sha bambam.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.