Kame Kame Gwamnatin Buhari Keyi, Ba Inganta Tattalin Arzikiba – Bill Gates




Mutum mafi karfin arziki da tarin kudi a duniya, Bill Gates, ya bayyana cewa tsarin inganta tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zayyana, kuma ta ke a kai, ba shi da karfin shawo kan dabarun inganta tattalin arzikin da Najeriya za ta bi ta kai gaci.
Gates, wanda shine mai kamfanin Microsoft, ya ce Najeriya za ta iya zabura ta cimma kasashen da suka habbaka sosai a yanzu irin su Brazil,China da Mexico, amma hakan ya dogara ne ga irin zabin da shugabannin kasar suka dauka su kai Najeriya a mafita.
Bill Gates yayi wannan jawabi ne a taron sanin alkiblar tattalin arziki da Majalisar Inganta Tattalin Arziki ta Kasa, NEC ta shirya a Abuja.

Ya ce kada shugabannin Najeriya su tsaya kawai ga gina ababen more rayuwa, a cikin al’umma, tilas sai an gina al’umma yadda za su rika zuba jari sannan tattalin arzikin kasa zai inganta kuma ya habbaka.

Ya ce Najeriya na kokari wajen ganin ta inganta tattalin arziki, amma magana ta gaskiya, yadda ake aiwatar da tsarin bai yi gam-da-katar da abin da al’umma ke ainihin bukata ba.
Gates ya ce, “idan ana gina ababen more rayuwa, to tilas sai ana tafiya a lokaci guda kuma ana gina al’umma.
Domin abin na tafiya ne kafada-da-kafada.
Al’ummar da ba ta da tituna da ingantattun tashoshin jirage masu kyau da kuma masana’antu baza su taba shahara ba.
Sannan su kuma tituna da tashoshin jiragen ruwa da masana’antu, idan babu kwararrun masu aikin da za su rika tafiyar da su, to tattalin arziki ba zai iya dorewa ba.”
Idan ba a manta ba, bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya hau mulki, ya kaddamar da Shirin Inganta Tattalin Arziki,ERGP (2017-2020).
Gates ya ce mafi muhimmancin turbar da ta dace Najeriya ta bi, ita ce “ta inganta babbar albarkar da take da ita, wato gina al’ummar ta.”
Ya ce Najeriya za ta zama kasaitacciya idan al’ummar ta sun zama kasaitattu wajen inganta kasar da kan su.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15