A makon da ya gabata mun tsaya wajen da SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA ya ke bayani kan sahabbai, inda ya ce sahabbai kashi biyu ne; akwai Mukhlisai akwai Munafukai. Don haka za mu cigaba da tattaunawa da ya yi tare da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, RABIU ALI INDABAWA , kamar haka:
Sahabbai iri biyu ne; akwai Mukhlisai muminai na Allah, wadannan su ne sahabbai na kirki, akwai munafukai. To, ni yakin da a ke da ni shi ne, cewa da a ke munafukan nan da Mukhlisan nan duk daya ne, sai na ke ga ba a yi wa Allah adailci ba, ba a yi wa manzon Allah ba, ba a yi ma sa biyayya ba. Kuma maganar nan ba ni kadai na yi ta ba. Malamai da yawa sun yi ta, iya abinda na fada ma rigimar nan da ta shiga ta mulki a cikin abin masu mulki a hannu su su ka aikata zaluncin nan, su ka binne al’amuran, su ka sayi malamai, sai abu ya taho a haka, wanda ya yi bincike zai gane gaskiyar abin kamar yadda ta ke faruwa yanzu. To, wannan gaskiyar idan ka fito da ita sai a ce ka zagi sahabbai. Na ba ka misalin wani sahabi da na yi bayaninsa, Jaddu Dan Kaisu. Jaddu Dan Kaisu idan ka ga abinda ya yi wa Manzon Allah, za ka yi kuka. Ko aya ba ta sauka kansa ba bai dace Musulmin kirki ya so shi ba. Ya yi wa Annabi wulakancin da ko ni ko kai a ka yi wa, ba za mu bari ba. To, har ya zamana wahayi ya sauko daga sama; la’ana 14 Allah ya yi ma sa. A cikin la’anar akwai dauwamarsa a wuta, amma ya na nan sun sa sunansa a cikin sahabbai a na ce ma sa ‘radhiyallahu anhu’; sun ce ya tuba, amma Alkur’ani karara Allah ya ce, ba zai fita daga wuta ba. Yanzu ya zama ya tuba? Kenan ka ga ba ma zai shiga wutar ba. Ashe kenan ka ga abinda Allah Ya fada ya zama karya kenan, kuma ita wannan maganar ta cewa ya tuba, ba Annabi ne ya fade ta ba, ba Allah ne ya fade ta ba, wani malami ne dan karnin tara kuma ba sahabi ba, ba tabi’ittabi’ina ba, a ka kuma dora jama’a a kai.
Yanzu na ke rabe ma su na ke cewa wannan Jaddu Dan Kaisun ba sahabin Annabi ba ne; munafuki ne, ya cuci Manzon Allah, ga yadda ta faru, ga abinda Allah ya ce kansa. To, ya jama’a ku daina ce ma sa ‘radhiyallahu anhu’, ga abinda Allah ya ce kansa. Sai a ce na zagi sahabi. Ni na yi zagi? An duba Kur’ani babu ayoyin nan? An duba, akwai. An duba an ga ba kansa su ka sauka ba? An duba an ga kansa ne, kuma Annabi ya canja wa ayar nan fassara yadda wadannan su ka yi? Za a ga bai canja ba. Haka sahabban, haka tabi’ai, sai da a ka zo karnin da a ka sayi malamai su ka canja maganganu su ke fada, wai an zagi sahabbai, mai daukar irin wadannan mutane da Allah ya la’ance su ya na sa su cikin sahabban kirki shi ne makiyin sahabbai, mai cewa a ware irin wadannan sahabbai a daina shigar da su cikin sahabbai shi ne masoyin sahabbai.
Saboda haka ni a ganina masu irin wannan burum-burum su ne makiya sahabbai, kuma makiya Allah ma a lambar farko, makiyan Manzon Allah ma a lamba ta biyu, sannan makiyan sahabbai a lamba ta uku. Ni a ganina wadannan su su ke zagin sahabbai, ba ni ba.
Akramakallahu duk malamin da ya kai mataki irin naka, ba a raba shi da tafiye-tafiye, la’alla karatu ko sayen littafi ko karbo lambar girma. A wannan gwagwarmaya, an je kamar kasashe nawa?
To, a gaskiya da yawa, sai wadanda zan iya tunawa a nan Afirka ta Yamma na je da yawa, makotan Nijeriya ba inda ban je ba. Tun daga Nijar ta nan kusa, kwanan nan ma zan je Nijar din, domin Ina da jama’a a cikinta. Chadi, Ina da masoya; Kamaru, Ina da jama’a; Ghana, Ina da jama’a; har su Kwatanon nan; Togo ne, su Mali, Burkina Faso, su Muritaniya. Kodayake Muritaniya ban je ba, amma wadannan duk na je su. A Afirka abinda zan tuna kenan, a Afirka ta Yamma. Ta Arewa kuwa, ka ga tun daga abinda ya yi Tunis, Libiya da Aljeriya da Moroko, duk wadannan ba inda ban taka ba a ciki. Idan ka yi gabas, Arewacin Afirka, Misra kenan, na ma yi tafiya a mota tun daga nan birnin Kano har Alkahira a mota.
Kuma abinda ya yi gaba nan ya shiga Iran, ya tafi Siriya, ya shiga Jodan, ya shiga Falasdin, ya tafi ya danna Fasha duk na shiga. Da ma Saudiya ba a magana wannan ta zama gida, ba za a iya sanin adadin zuwan da a ka yi ba. To, amma duk da Malesiya, haka Ethiopia, su Mozambik, su Japan, su Kuwait. Wannan duk Allah ya nufa na je su, kuma duk a kan wannan hidima ta addini. Idan ka dawo irin su Rasha din nan, abinda ya kama a cikin Asia, amma Sudan kam an je ta ba adadi. Har Turai na je Holland, na kuma je bangaren Amurka, a ciki na je New York, na je Sam Francisco, na je Los Angeles. To, wadannan dai duk na je su a wadanda zan iya tunawa, na shiga kasashe da yawa a gaskiya.
To, ya zuwa yanzu Malam ya wallafa littattafai kamar guda nawa?
Ba zan iya rikewa ba, amma ko wadanda a ka buga dai goma sha ne, wadanda na rubuta ba a buga ba sun fi 20, wadanda na ke kan alkawarin bugawa na rubuta har na yi masu littafi, wato ‘Kurratul’a’ayun’, Ina jin idan ka ce a tara da wanda a ka buga da wadanda na gama rubuta su su na shiri yanzu a nan a na son a buga su da wadanda na yi alkawarin zan rubuta su, amma ban rubuta ba su na tafe, ai lallai sun fi 100. A samu sama da littafi 100, kuma a cikin 100 din nan akwai wadanda na yi nisa a ciki na kai Mujalladi wato (Bolume) zai kai hudu, ba a buga su ba hudun nan, kamar rubutun hannuna su na nan na rubuta, kuma ba zan gama su ba sai ya tafi wajen Mujalladi 20, amma a daya ya ke.
Ka ga idan da kowanne mujalladi za a yi ma sa suna an samu littafi 20, kuma manya-manya ne, dibga-dibga ne; ko wane daya za ka samu shafi 700, 800 a ko wane daya. To, kuma 700, 800, din nan su za ka kirga daya biyu uku hudu biyar har littafi 20 kuma duk littafi daya ne, sunansa ‘Tahkeekul Munya Bi Sharhi Kitabul Gunya’. a yanzu dai zai yi mujalladi hudu abinda na yi, kuma ba haka kawai na kirkire su ba, saboda ba lokaci. Akwai ‘Jauful farah’, wanda na fara bana a tafsiri. Shi kuma yanzu abinda na rubuta ya yi mujalladi, shi kuma mu na kaddara cewa shi ma zai yi mujalladi 20. To, yanzu ka ga 40 ta samu a littafi biyu. Yanzu ina da bugagge ‘Mukaddimatul Azufah’; mujalladi uku ne. Na yi biyu Ina cikin na ukun, littafi daya ne suna daya ne da shi, amma mujalladi uku ne, kuma ba wai kanana ba, za ka samu mai shafi kusan 800 shi kadai.
Yanzu kwanan nan na rubuta ‘Al’ababil’. Shi ma shafi 800 ne, shi din ma guda biyu zai zo, amma na yi daya saura daya. To, a fa wannan goma sha din da na ke gaya ma ka akwai wanda a wannan ban saka su ba, kuma a darin ma da na fada ma a haka lissafin ya ke. Ba wai Ina nufin idan na ce mai mujalladi 20 za a sa 20 din a lissafi ba ne, a’a, sunansa guda daya za a sa a lamba. Ina fata ka fahimta. Idan an ce ‘Tahkeekul munya’, shikenan ba za a sake maimata sunan sau 20 ba; kwaya daya za a ambata a wuce, daidai da wanda zai ma littafi yanzu shafi goma. Ka ga akwai littattafai da a ke yi shafi 10, shafi 30, sai a yi masu suna kuma sunansu littafai. Mai mujalladi 20 din nan littafi, mai shafi 20 littafi.
To, saboda haka alhamdu lillah; a yanzu rubuce-rubucen nan da mu ke yi za su ba ka sha’awa, Malam Rabiu, kawai matsala ta rashin isasshen lokaci, saboda hidimar da yawa.
Ni ka ga wadannan teburan nawa da ka ke gani, takardu ne a kansu kawai da littattafan tarihin da na ke akwai wasu rubutun kawai su ka yi har su ka mutu, wasu kuma yawon wa’azi su ka yi, wasu makaranta su ka kafa ba a zuwa ko’ina sai dai a zo a dauki karatu, wasu ta daidaiku su ke ba ta darasi haka na jam’i ba, wasu kuma Allah ya dora masu hidindiminsu na ammara abinda ya shafi assasawa, kamar masallatai su ke samarwa da makarantu, wani masallatan kawai ya ke, bai dai wani abu da ya assasa sai masallaci.
Amma alhamdulillahi ni abinda ya dankare min wuya, duk bangarorin nan ba wanda Allah bai kaddara min ba. In gina makaranta yau, na gina masallaci, na bude Rawiyyah, na bude Zawiyyata, na wallafa littafi, na yi karatun jam’i, in na daidaiku in yi tafiya. Kari a kan wannan kuma a ka jarrabe ni da hassadar mutane masu kunno min wutattaki. Yau sai ka jini kawai an kai ni kotu a na shari’a ba gaira ba dalili, gobe an kwace min masallaci a na kes da ni, jibi ’yan sanda su na nema na babu gaira babu dalili, kuma idan an bincika daga karshe ka ji babu wani abu. Me ka yi wa ’yan sanda? Babu. Me ka yi wa wannan ya kai ka koti? Babu. Me ka yi wa wancan ya dira masallacinka? Babu. Me ka yi wa wancan ya shirya majalisi ya zazzage ka ya yi kaset? Babu, Me ka yi wa gwamnati can ta ke ta kulle-kulle a tade ka? Babu. Babu wata gwamnati da ta ke tafiya da ni.
Kadai wannan ya ishe ni tarnaki, domin a irin wannan aiki na malantaka ya na bukatar dafawar masu madafun iko, kamar gwamnati, iri na dafa min za a yi, musamman in an dubi duk abinda ya zo shiga aljihun gwamnati da a ke cewa ‘grant’ din nan sai da a ka kirga su da nasu a ciki, kuma ba laifi daya da a ka fito da shi na yi.
Ka ga Ina da cikakken hakkina a matsayina na dan kasa dan jiha, dalibaina ’yan kasa ’yan jiha. Idan da cibiyoyin nan nawa da na ke da su ta’addanci a ke koyarwa da tuni Kano ta kusa tashi yanzu. Ashe da ya zama akasi a ke koyarwa, ka ga kenan taimakawa Kano a ke yi. Wani misali zan ba ka mai ban sha’awa. Wani dan makaranta ta ya zo har gida ya yi min wannan albishir din, ya ce, Akramakallahu wannan wa’azin da ka ke yi wajen nunawa mutane jin kai da tausawa ’yan uwansu ba ni adama ya na tasiri, kuma bari in yi ma ka albishir. Jama’ar gari ma sun fara gane dalibanka da irin wannan dabi’ar ta wa’azin da ka ke masu na jinkai, su na ta gwada jinkan har a gari wasu na iya gane dalibanka.
Ya ce ta faru kaina yanzu, mutum ne mashin dinsa yam utu, na jingine mashin dina Adaidaita sahu, na yi ta tura masa nasa sai da ya je ya ajiye na zo na dauki mashin dina. Za mu yi sallama ya ce kai bawan Allah, don Allah zan yi ma tambaya in ji dai ba za ka damu ba, in ji dai kai almajirin Malam Abdujjabbar ne? Wani abin mamaki, ya ce, ya a kai ka gane? Ya ce ah, ai dalibansa haka suke, suna da jinkai, suna da yakana, y ace ta faffaru gareni, in ji mai Adaidaita Sahu, ranar sai na ji kamar in zuba ruwa a kasa in sha a kasa don murna, sai na ji kamar wahayi aka yi min. Saboda me abu ne da ya faru a gari can wata shaida, shi ne abinda yake fada masu “Ku dai ku yi gaba da batan mutum ka da ku yi gaba da mutum, ku jikan mutum ku tausaya masa, dan Adam abin a tausaya masa ne ko Kafiri ne, ka inda aka ce a yi gaba, zubar jinni a Musulunci shi ne mataki na karshe wannan kalmomin ashe suna karbuwa a gun dalibaina, sai ga albishir an kawo min, to wanda yake da wannan shaidar, in har gwamnati da gaske take tana kyakkyawan tsari ya kamata ta fi kowa sanin haka, dan Adaidaita Sahu dai ya gano abinda gwamnati daga bangare na SSS wanda aikinsu ke nan su bazama su gane me yake faruwa a cikin al’umma, amma ba ta san wannan ba, ka ga sai ya zama bata cancanci ta zama gwamanati ba, koko ta san wannan ta ta ke kuma ake yakar wanda yake yin wannan, da da’awar karya cewa yana zagin Sahabbai zagin da har yau babu, amma a kasa ga shi yana yi wa al’umma aikin da har yanzu ana shaida dalibansa da ban acikin mutane, wannan Allah ba zai bari ba.
Kuma wani abu mai ban mamaki babu abunda ya hada mu rigima da gwamnati ko ta mutum da mutum ko ta siyasa, a yanzu haka babu wata adawa da na kewa gwamnati, ko gaisawa ba ta hada ni da su, balle mu tattauna wata mas’ala ta gwamnati balle in shiryar da cutar da ita. Abin nan da ka gani ka zo ka same ni ina yi in na shigo gun nan, sai in kwan bakwai wani lokacin wallahi daga Juma’a sai Juma’a na ke fita, Ina cikin littattafai. Me ya ke faruwa a cikin tsakiyar makarantar nan, wallahi sai faru sau kaza ban sani ba, balle me ke faruwa cikin Gwale, balle me ke faruwa cikin jihar Kano, balle me ke faruwa a gidan gwamna. Ka na nan sai dai ka ji an dauko bam an wurgo ma ka. Me ka yi? Ba ka sani ba. Saboda haka don Allah ku a matsayinku na ’yan jarida ku taimaka ma na ku dinga isar wa da hukumomi irin wannan sakonni. Ba daidai bane a ce gwamnatin da za ta gina al’umma, ta dinga rusa ta.
Za mu cigaba a makon gobe idan Mai duka Ya kai mu.
Comments
Post a Comment