Masoyana Za Su Ga Canji A Dawowa Ta Harkar Fim –Abba El-Mustapha





Fitaccen jarumi ABBA EL-MUSTAPHA ya dade ana damawa da shi a masana’antar finafinai ta Kannywood wanda kuma mai shirya finafinai ne, ya dade yana sharafinsa a can baya sai dai kuma lokaci guda aka daina ganinsa in ban da a wannan lokacin da ake ganin sa a cikin manyan finafinai ganin cewar duk wani jarumi da ya ta fi an daina yayinsa ke nan, amma shi Abba da ya dawo sai kuma ya ke nema ya wuce jaruman da ya tarar a wajen. Don haka ne LEADERSHIP A YAU LAHADI ta ji ta bakinsa a game da shirin da ta yi wa dawowar ta sa. Sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance:
To Abba Almustafa kai jarumi ne da ka dade a cikin harkar fim in banda a lokacin baya da aka daina ganinka sai kuma a wannan lokaci da ka yi wata irin dawo wadda ta girgiza jaruman da ake harkar da su a yanzu.

To da farko dai tunda zan fara fim na fara ne da sunan Allah kuma nake fatan na gama da godiyar Ubangiji, don haka nake ganin wannan shi ne tushe da kuma tasirin nasara ta don haka lokacin da na shiga harkar fim mun dau lokaci ana damawa da mu a cikin harkar, kuma an samu daukaka da nasarori da dama a wancan lokacin kuma lokaci ya yi da muka ga cewar sai mun ja gefe, amma dai kamar fada da rago ne da ake cewa, ja da baya ba tsoro ba, haka jan baya da na yi ba yana nufin na tafi ke nan ba. To yanzu da lokacin dawowar tawa ya yi sai na ga shi na dawo, kuma cikin nufin Ubangiji sai ga shimun zo mun dora daga inda muka tsaya kuma sai masana’antar ta karbeni fiye da yadda nake zato ma, wannan kuma yana da alaka da zaman lafiyar da muka yi da mutane, don haka a yanzu na dawo na dora daga inda na tsaya.

A can baya a na ganin kamar karfin kamfanin ka ne ya sa a ke gayyatar ka, amma a wannan dawowar sai ka dawo a matsayin jarumi kuma masana’antar ta karbe ka.

To, abin da ya sa ake ganin haka shi ne, a wancan lokacin na fi ba da karfi a wajen shirya finafinai don haka ko da an gayyaceni fim ina duba tsari na ne don haka ba kowa nake yi wa fim ba don haka na fi ba da karfi a nawa kuma sai ya zama mutane sukan zo suba da kudi na shirya musu amma yanzu na dawo ne a matsayin jarumi sai kuma masu shiryawar suka ga ai akwai wani gibi da na bariwanda har yanzu ba a cike shi ba don haka sai na samu damar dorawa daga inda na tsaya duk da cewar ba a yanzu na yi niyyar dawowa ba sai ga shimasoya da furodusa da suke cewar yanzu ne ya kamata na dawo din don haka a yanzu ina matsayin jarumi ba furodusa ba don haka duk wanda yake da dama ko labarin da ya shafeni to a yanzu ne ma ya kamata ya zo mu yi harka da shi kuma a wannan yanayi ina godiya ga abokan sana’ata a game da karba ta da suka yi bayan tsawon lokacin da ba na yin fim.

Hakan ya nuna a wannan dawowar ta ka ba ka da niyyar shirya fim na kamfaninka ke nan?
To, ai kamar yadda na fada a baya nace, na dawo yanzu a matsayin jarumi kuma hakan ba zai hana ni shirya fim na kamfanina ba domin a yanzu ma akwai finafinai da nake so na shirya amma ban saka lokacin ba. Ina nan dai na shiri da kuma gyaran labarundon haka a wannan dawowar tawa sabon abu za a gani.

To a dawowar da ka yi ita masana’antar ta samu canji na jarumai da masu shiryawa da mafi yawa bayan tafiyar ka suka shigo, ko yaya ka samu kan ka a wajen mu’amala da su?
Ai ni ina ganin ita mu’amala abu guda ne, idan ka iya za ka zama ka yi daidai da kowanne zamani, don haka ko da na dawo naga harkar a yawanci daga wandanda aka raina sai abokan kannenka sai yaran ka na baya to yanzu sai ya zama babu wani abu sai girmamawa a tsakanin mu kuma ni ci gaban harkar fim ce a gabana a kodayaushe don haka wannan kaunar junan da ta ke tsakanina da su hakan ya mayar da ni kamar ba bako a cikin suba.
A yanzu da ka dawo me ya fi daukar hankalin ka a masana’antar?.

Ni ina ganin abin da ya fi daukar hankali na abu biyu ne, ingancin labari, na biyu kayan aiki ya canja ba kamar yadda na sani a bay aba. Sai na uku kuma an samu kwarewa a cikin harkar don ana tafiya neman ilimi game da sana’ar kuma ana fadada neman hanyar kasuwancin fim da yadda zai habaka,kuma dai a yanzu muna neman gwamnati ta kara shigowa a cikin harkar kamar yadda muke ba su gudunmawa su ma su zo suba mu ta su gudunmawar don haka a baya an ce za a yi mana Alkayar fim kuma abin ya zo ya samu matsala to idan ma ba a yi manaba muna so a mayar da kudin zuwa wata harkar da ta shafi fim don kuwa duk wata gwamnatin siyasa da ta ke zuwa ta na samuwa ne tare da gudunmawar ‘yan fim don haka muke rokon su da cewa ya zama dole su zo su taimaka wa harkar tunda ta matasa ce wadda dunbun jama’a suke cin gajiyar ta.

Da ka yi maganar siyasa, an san cewa azaben da ya wuce ka yi siyasa har ma ka tsaya takarar majalisar wakilai a yanzu gashi ana shirin shiga kakar siyasa, ko a wannan karon ma za ka sake tsayuwa?

To, a kullum ina rokon Allah ya zaba mini mafi alheri a rayuwata, na yi takara a 2015 ta dan majalisabisa nema na da jama’ar karamar hukumata ta Gwale suka yi kuma na yi Allah bai ba mu nasara ba don haka na samu kwarewa kuma na fahimci shi dan fim idan ya rike mutuncin sa to babban mutum ne a cikin jama’a. Amma a 2019 ba zan iya cewa zan yi takara ba sai dai muna rokon Allah ya zaba mana abin da ya fi alheri, ina rokon masoyana da su tayani da addu’a.

To mene ne sakonka na karshe?
Sakona na karshe, ina so na yi kira ga masoya masu kallon mu su kara ba mu hadin kai wajen yakar masu satar fasaha don jari muka sa muka fito da shi mu yi abin da za mu faranta musu rai don haka muna so su ta ya mu wannan yaki na masu satar fasaha don fadan ya fi karfin mu sai sun shiga sun taya mu, mu hada kai.
To madalla, mun gode.
Ni ma na gode.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15