
Wani dan bautar kasa da ba a bayyana sunan shi ba tukun ya dirkawa daliba mai shekaru 11, ‘yar aji biyu a sakandire cikin shege.
Dan bautar kasan na yi wa kasa hidima ne a Warri da ke jahar Delta inda a nan ne lamarin ya faru.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da iyayen yarinyar suka dauki dan bautar kasan aikin koyawa yarinyar karatu a gida.
Yarinyar daliba ce a makarantar Nana College da ke Warri.
Yanzu haka dan bautan kasar na hannun jami’an ‘yan sanda, haka zalika an aika rahoto ofishin hukumar NYSC domin ta dau irin na ta mataki akan shi.
Comments
Post a Comment