Wani likita a asibitin gwamnatin tarayya da ke Abuja, Dakta Zayad Ahmed ya gargadi mutane da su guji kwanciya da zaran sun kammala cin abinci, saboda wannan dabi’a na haifar da matsalolin ciki da dama.
Likitan ya fadawa kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN cewa dabi’ar ita ke haifar da ciwon ciki da rashin narkewar abinci.
Ya ce an tsara jikin dan adam ne ta yadda zai iya narkar da abinci a zaune ko tsaye ba a kwance ba, kuma bai kamata a yi abunda ya saba wa wannan tsari ba.
A cewar shi, ” Mutane su kiyaye da abunda zai iya haifar masu da ciwon ciki”
Likitan ya kuma yi gargadin a guji cin abinci da yawa a lokaci daya, inda shi ma abu ne da ke haifar da matsaloli. Ya ce mutane su jimirci cin abinci daidai wadaidai a kowanni lokaci.
Shawarwarin shi na karshe su ne. mutane su rage cin abinci mai dandano da yawa da wanda mai ya masa yawa, saboda su na iya haifar da zawo ko rashin narkewar abinci, inda haka zai iya haifar da murdewar ciki.
Sai kuma game da cin nau’ikan abinci kamar su wake da waken suya, wanda likitan ya ce ke haifar da iska a ciki da sauye-sauye a yadda cikin ke gudanar da lamuran shi.
Likitan ya shawarci jama’a da su jimiri motsa jikin su domin su kasance cikin walwala da rashin gajiya a koda yaushe.
Comments
Post a Comment