Da Zan Zama Shugabar Nijeriya Sai Na Hana Alfarma –Maryam Turau




An fi sanin MALAMA MARYAM NUHU TURAU a fagen rubutun littattafan Hausa, amma kasancewar ta mai lura da al’amuran yau da kullum a kasa, musamman siyasar Nijeriya, Turau ta na da damuwa kan yadda alfarma wajen tafiyar da Nijeriya ke hana ruwa gudu da kuma yadda ’yan siyasa ke amfani da matasa wajen tayar da zaune-tsaye a lokacin zabe. Ga dai yadda tattaunawarta da wakiliyar LEADERSHIP A YAU
LAHADI, FADILA H. ALIYU KURFI , ta kasance:
Ko za mu iya jin takaitaccen tarihinki?
Sunana Maryam Nuhu Turau. An haife ni a Katsina a cikin unguwar Rafindadi. Na yi firamare a Rafindadi Model Primary School, wacce a ka maida Waziri Zayyana Science Model Primary School a yanzu. Na je sakandare a makaranyar ’yan mata ta WTC na yi karamar sakandare daga daya zuwa uku, sannan na koma Unity Girls College (edchange school) na ida SS 1-3. Na yi NCE a FCE Katsina na karanta Primary Education Hausa. A bangaren addini kuma na fara tun Ina ’yar sheka hudu a makaranyar allo sai da na yi sauka ta ta farko sannan a ka saka ni Islamiyya.

Mene ne asalin fara rubuce-rubucenki, sannan kuma ya zuwa yanzu littafi nawa ki ka fitar?
Asalin fara rubuce-rubucena ya samu asali daga karatun littafin irinsu Magana Jari Ce da a ke ba ni Ina karantawa lokacin Ina makarantar firamare kasancewa ta wadda na fi kowa iya karatun Hausa a ajinmu. Ya zuwa yanzu na rubuta littattafai da dama, amma biyu ne kawai su ka shiga kasuwa.

Me ya ja ra’ayinki har ki ka fara rubutu?
Zan iya cewa yawan karatun littattafai ya sa na fara sha’awar rubutawa har Allah ya ban ikon zama marubuciya.

Wane hasashe za ki yi game da siyasar Nijeriya da makomarta?

A da siyasar Nijeriya siyasa abar kyama ce, domin a wancan lokacin a na tsara zabe a kuma aikata shi ba bisa ka’ida ba. Dan takara zai iya yin komai, ciki har da kisa, don ya ci zabe. To, alhamdulillahi, yanzu an samu cigaba sosai a siyasar Nijeriya, wanda idan har a ka dore a haka kasar nan za ta iya kaiwa wani matakin da za a rika koyi da ita.

Me ki ka fahimta bambanci tsakanin siyasar ra’ayi da siyasar neman mukami?

Siyasar ra’ayi siyasa ce da a ke yi domin kawo cigaban kasa. A kan nuna kishi da jajircewa, domin a kawo gyara da kuma cigaba. Duk mai irin wannan siyasar ba ya neman dole sai shi ne zai zama mai mukami ba, sai dai ya ga ta ina za a yi gyara, ta ina za a samu cigaba da duk wani abin alkhairi. Ita kuwa siyasar neman mukami siyasa ce da a ke yi kawai don cikar buri; siyasa ta handama da babakere, siyasa ce ta son kai, rashin kishi da rashin taimakon talakkawa, siyasa ce ta wargaza kasa da kashe ’yan kasa. Mutum zai yi duk abinda zai yi ya dare mulki ya kama madafun iko ya karkame su a hannunshi. Komai zai yi, zai yi ne, don ra’ayin kanshi, ba ruwanshi da gyaran kasa bare talakkawan da ke tsugune karkashinsa.

Meye makomar matasa a mahangarki game da siyasar kasar?

Babu masu ban takaici a siyasar kasar nan sai matasanmu da ba su san kansu ba har yanzu. Wai yaushe matasanmu za su farka su dawo cikin hayyacinsu ne? Yaushe matasanmu za su bar zama karnukan farautar ’yan siyasa? Har idan matasanmu ba su dawo hayyacinsu su ka bar bangar siyasa ba, ba za su rasa makoma mai kyau ba. Matasa na da matukar mahimmanci sosai kuma za su iya taka kyakkyawar rawa a harkar siyasa, amma idan har ba jagaliyar siyasa a ka jefa su ba. ’Yan siyasarmu su bar bata rayuwar matasanmu, su rika taimaka ma su wajen samun ingantaccen ilimi, don su ma su zama wasu a gobe.

Shin ko manyan Nijeriya na yin wani yunkuri, domin tallafa wa matasa ko kuwa dai su na tayar da mota ne ta bade su da kura?

Tam! Babu wani kokari da manyan kasar nan ke yi, don inganta rayuwar matasan da su ka taimaka ma su har su ka dare kujerun mulki. To, wai ma ina matasan su ka gan su? Wani ma daga ranar da ya ci zabe ya tattara iyalinsa su ka haura Abuja, ka gama ganin shi ko muryarshi ka gama ji sai dai idan ka dace wata rana ka gan shi a talabijin ko ka ji muryarshi a gidan rediyo a na hira da shi. Da matasanmu za su gane, su bar wahala da kashe junansu a kan ’yan siyasa.

Wacce gudunmuwa matasa za su iya bayarwa wajen cigaban siyasa ko dimukradiyyar kanta, idan damar hakan ta samu gare su?

Ba don kar a ce na cika baki ba, da sai na ce, matasa na iya canza Nijeriya idan har su ka samu taimako a ka inganta rayuwarsu da ilimi, kasancewar su su ne kashin bayan al’umma kuma su ne ma su jini a jika da a ke hangen kamar yanzu su ka fara rayuwa. Da za su samu dama, tabbas da an sha mamaki.

Ko a kasar Katsina mata na shiga a dama da su a siyasance ko kuwa su ma su na komawa baya su nade hannu su zama ’yan kallo ne?

Har yanzu kan mata a Katsina bai ida waye ba sosai ta fannin siyasa ba. Kalilan ne ke fitowa. Su ma za ki ga ba neman wani mukami su ke fitowa ba, sai dai su raka yarima a sha dadin kida. Mu na fatan nan gaba kadan mata su fara fitowa a na gogawa da su.

Da za ki yi mulki a Nijeriya, wane abu ne za ki fara yunkurin gyarawa?

Alfarma ce farkon abinda ke ci min tuwo a kwarya. A Nijeriya ne za ka ga wanda bai cancanta ba ya rike wani mukami, saboda ya na da alfarma, amma ga wanda ya cancanta ba za a ba shi ba, saboda bai da kowa. Don haka na ke adawa, bakar adawa! da alfarma. Sai cin hanci. Wannan na san ba ni kadai ba, duk wani mai kishi zai yi fatan ganin karshen numfashin cin hanci da rawa. Sai inganta rayuwar matasanmu. Ina mai mafarkin ganin rayuwar matasanmu ta inganta ta hanyar da za su zamo shugabanni nagari a gobe, sannan ilimi. Zan gyara harkar ilimi ta yadda zai zamo ingantacce. Kowa ya sani a Nijeriya mu na da albarkatun kasa da shugabanni ba su damuwa da su. Zan yi kokari gyara wadannan albarkatun har sai ya zamo mu na gogayya da manyan kasashen da su ka cigaba da yardar Allah.

Wane kira za ki yi ga shugabannin duniya kan yadda su ka dauki siyasa ko mulki tamkar gado?

Wannan halin nazari da dogon buri a kan kujerar mulki ya kamata shugabanninmu su farka. Shugabanci ba mulkin sarauta ba ne, wanda za ka ce idan ka hau ba ka sauka har sai ka mutu a kai. Ya kamata idan ka yi wa’adinka ya cika ka sauka wani shi ma ya gwada irin nashi kokarin.

Daga karshe wacce shawara za ki ba wa matasa?
Shawarar da zan ba su ita ce, don Allah su san kansu, su taimaki rayuwarsu su ingantata ta, su bar bangar siyasa, su nemi sana’ar da za su dogara da kansu. Ina yi wa matasanmu fatan alkhairi. Na gode; ni ce
maryamturau@gmail.com.

Premiumtimes Hausa

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15