Hawaye sun kwaranya yayinda aka binne jaruma Hauwa Maina

An sada jarumar shirya fina-finan Hausa Hauwa Maina da gidanta na gaskiya.
Anyi jana’izar jarumar ne a jihar Kaduna, a yau Alhamis, 3 ga watan Mayu.
Shafin Kannywood ta wallafa hotunan jana'izar jarumar.
Kamar yadda muka kawo a baya, marigayiya Hauwa ta rasu ne a wani asibiti dake jihar Kano.
Ta rasu ne a daren ranar Laraba, 2 ga watan Mayu bayan tayi fama da jinya.
Comments
Post a Comment