A bisa zance mafi shahara an ce, wani mai suna Kumayo ne shugaba na farko a Katsina ko kuma ta na iya yiwuwa shi ne wanda ya kafa garin na Katsina ma kacokam. Sai kuma sarakuna masu suna Ramba, Taryau, Jatinnati da Sanawu su ka biyo bayansa a mulki (tsawon mulkinsu gabadaya kimanin shekaru 350). An ce, Sanawu ya shafe tsawon shekaru 30 a kan mulkin Katsina, sannan a ka ce Korawa ne su ka kashe shi, wasu al’umma kenan da su ka zo daga ‘Yantandu su ka kafa daular su a Katsina. Su ne su ka damka jagorancin Katsina a hannun Sarki Ibrahim Maji. Watakila hakan ya auku ne a wajejen shekara ta 950 bayan hijira. Sannan an samu cewa, shekaru 30 kafin zuwan Ibrahim Maji a mulki (wuraren shekarar 1513 miladiyyaa, 919 hijiriyya), dakarun Sarkin Songhay Alhaji Muhammadu Askia sun kwace garuruwan Hausa gabadaya ciki har da Kano da Katsina. Kamar yadda wasu su ka ruwaito sun ce, lokacin Katsina na karkashin ikon birnin Kano ne kuma garuruwan biyu sun shafe lokaci kalilan ne a karkashin daular ta Song