To tuni dai aka bayar da kyaututtukan girmama ga wasu zaratan ‘yan wasa da suka taka rawar gani a gasar cin kofin duniyar da ta karkare jiya lahadi a Rasha.
Jagaba a ‘yan wasan bayan kasar da ta lashe kofin Faransa da Croatia da ke matsayin ta biyu da kuma Belgium a matsayi na 3, akwai Harry Kane dan Birtaniya.
Dan wasan na Ingila Harry Kane ya lashe takalmin zinare kan kwallaye 4 da ya zura a raga kuma ita ce kyauta mafi daraja bayan kasashe na daya dana biyu da kuma na uku.
Harry Kane dai shi ne dan wasan Ingila na farko da ya lashe wannan kyauta ta takalmin zinare a gasar cin kofin duniya tun bayan Gary Lineker shekaru 32 da suka gabata.
A rukunin ‘yan wasan da suka zura kwallaye hur-hudu a raga kuma akwai Cristiano Ronaldo dan Portugal mai shekaru 33 sai Antoine Griezman na Faransa da Kyllian Mbappe shima dan Faransar sai kuma Danis Cherysheb dan Rasha da Romelu Lukaku dan Belgium.
Rukunin ‘yan wasa masu kwallaye 2 kuma wadanda suma suka samu girmamawar akwai Edinson Cabani na Uruguay da Costa dan Sipaniya da Dzyuba dan Rasha da Hazard dan Belgium da kuma Mandzukic dan Craotia da Mina daga Colombia da kuma Perisic shima dan Croatia.
A rukunin ‘yan wasa masu kwallaye bibbiyu ne aka hango keyar ‘yan Afrika, irinsu Ahmad Musa dan Najeriya da Muhammad Salah dan Masar da Khazri dan Tunisa.
Sauran masu kwallaye bibbiyun akwai kuma irinsu Neymar, da Suares da kuma Modric.
Comments
Post a Comment