An Nada Rarara darekta waka na kamfen din Buhari 2019




Fitaccen mawakin siyasa da ya shahara wajen yi wa shugaba Muhammadu Buhari waka ya zama sabon darektan waka na kamfen din Buhari.
Bayan shi a kwai fitaccen mai shirya wasan kwaikwayo na Nollywood, wato Desmond Elliot a kwamitin.
Kwamitin da tsohon gwamnan jihar Barno sanata Ali Modu Sheriff zai shugaban ta na tattare da jiga-jigan ‘yan jam’iyyar APC da take bugun kirji da su.
Kamar yadda PR Nigeria ya ruwaito wannan kwamiti da bam yake da kwamitin da ministan Sufuri Rotimi Amaechi ya ke jagoranta.
A kwamitin akwai, Mamman Daura, Boss Mustapha, Bola Tinubu, Matthew Mbu, Ahmed Sani, George Akume, Abdullahi Adamu, da sanata Ita Giwa.
Sauran sun hada da Honarabul Gudaji Kazaure, Ireti Kingibe, Ismaila Funtua and Abu Ibrahim.
Shi kansa shugaba Buhari na cikin wannan sabuwar kwamiti.

Comments

Popular posts from this blog

BRIEF BIOGRAPHY OF SHEIKH IBRAHIM AHMAD MAQARY, IMAM OF NATIONAL MOSQUE ABUJA

Wane Ne Sheik Abul Fatahi Maiduguri? Karanta cikakken tarihin sa

TARIHI: ZUWAN TURAWA KASAR HAUSA DA YADDA SUKA CI KANO DA SOKOTO DA YAKI A SHEKARAR 1903.