Mun Tsaya Takara Ne Don Samar Wa Da Matasa Ingantacciyar Rayuwa –inji Ahmad Sulaiman




Fitaccen malamin nan da ya yi fice a karatun Alkur’ani mai girma Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim ya shiga sahun siyasa na tsayawa neman takarar wakilcin majalisar jiha ta Tarauni bisa burin da yake dashi na ganin an kyautata rayuwar matasa wanda sune kashin bayan ci gaban kowace al’umma.
Da yake zantawa da jaridar Leadership A Yau a Kano, Malam Ahmad Sulaiman ya bayyana cewa dalilin da yasa ya fito neman takarar shi ne irin damuwa da yake da ita game da halin da matasa suke ciki dan ya sami dammar ya sa Gwamnati tayi tanadi na musamman na tsamosu daga halin shaye-shayen miyagun kwayoyi a gyara musu tarbiyya ta dawo dasu kan hayyacinsu da dorasu kan turba rayuwa mai kyau da kowa yake bukata.
Ya kara da cewa ta tsaftace harkar siyasar matasa ta yanda duk wanda zai fito takara ya zama mai niyya mai kyau a bashi dama ya aiatarda niyyarsa,saboda abinda ke faruwa yanzu komai kyan niyyar mutum sai ya zama ta gurbata saboda yanda matasa suka dauki harkokin siyasa a matsayin sana’a wanda ita kuma harkace ta wani dan lokaci idan akayi zabe ya wuce sai wani lokacin kamar yanda ake a wasu kasashe da suka cigaba zaka samu kowa ya koma kan sana’arsa.
Malamin yayi nuni da cewa idan za’ace ita siyasa itace sana’ar matasa,akwai matsala domin zababbbe idan ya fito neman takara wadannan matasan irin wahalarda yakesha a hannunsu takan hanashi dammar aiwatarda abubuwanda yakeson aiwatarwa saboda wahalarda yasha shi zaiga cewa sai ya maida wahalar kafin yace zai saurari wani abu.
Malam Ahmad yace yanaso yaga matasa sun sami abinyi,ba’a hana ayi siyasa ba,amma ya zama in anyi siyasa an gama zabe kowa ya tsaya a bakin sana’arsa.Yace idan kanaso ka kawo gyara a abu kamar yanda shari’a tace shine idan kaga abinki ka dakatar dashi koka rageshi ko ka tsai dashi.kamar yanda Annabi yayi umurni ka tsaida barna koka rage koka hanata yaduwa saboda haka abnda zai faru zaiyi kokari in yaje majalisa wajen bullo da tsare-tsare na matasa wadanda ke cikin harkar siyasa a tsamosu daga shaye-shaye dan bai kamata idan mutum yana neman mukami yasa ya’yan mutane a shaye-shaye ba,kamata yayi ya gyara wanda ya samu ya lalace wannan abinda zaiyi kokari akai kenan.
Malam Ahmad Sulaiman ya ce, a wannan takara tasa ba abinda zai cewa mutanen karamar hukumar Tarauni sai godiya domin yan takara su suke zuwa neman mutane,amma shi jama’a ne suke zuwa suna kawo kansu daga unguwanni daban-daban.Jama’ar Tarauni sunai masa kyakkyawan zato kuma da ikon Allah zai kaishi ga nasara.
Ya ce, Allah shi yake bada mulki duk abinda wani ya zama Allah ya lamunce masa su basuda komai na Dukiya lamuncewar Ubangiji suke nema dan jam’a suna kaunarsu sunada kyakkyawan zato akansu yana fatan samun taimakon Allah tareda rokonsa ya huwace masa.
Ahmad Sulaiman wanda dan jam’iyyar APC ne ya bayyana gamsuwarsa da salon mulkin shugaba Buhari da Gwamnan Kano Ganduje duk kuwa da craw ba’a iya samun mutum ya cika 100 bisa 100 sai an sami wanda zaice mulkin bai masa ba wannan kuwa ba wani abu bane tunda mazon Allah ma ya rayu a Duniya yafi kowa komai amma samada rabin Duniya basu bishi ba,duk da sunsan yafi kowa gaskiya,amana karamci.Saboda Duniya kasha biyune akwai mutanen kirki akwai akasin hakan duk inda mutum yakai ga kirki akwai wanda baya sonsa abinda ke faruwa kenan gameda mulkin APC a kasarnan Gwamnatice mutumin kirki ke jagoranta zai cigaba da fama da mutanen banza dan mulkinda Buhari yake a Najeriya da yanda ya karbi kasarnan an taka rawar gani sosai wajen dorata a turbar cigaba kuma za’aga fiyeda haka musamman idan Buhari ya wuce,shima Gwamna Ganduje ya wuce za’a ga abubuwa na cigaba kari akan abubuwanda ake gani yanzu.

Malam Ahmad Sulaiman Ibrahim yayi kira ga al’ummar Tarauni dana jahar Kano da kasa baki daya da cewa duk lokacinda za’ayi zabe su kalli mutum su duba su zabi mutumin kirki wanda zai kare musu hakkinsu kar suyi mummunan zabenda zai zame musu matsala daga baya a a basu wani abu kadan azo a bautar dasu daga baya tareda fatan zasu baiwa Buhari da Ganduje dammar maimaita mulkinsu shi kuma su bashi dammar samun nasarar zama wakilin karamar hukumar Tarauni a majalisar dokokin jihar Kano.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15