Dharmendra na daya daga cikin jaruman fina-finan kasar Indiya da suka yi fice saboda irin rawar da suka taka. Jarumi ne wanda ya yi suna wajen fina-finan fada, da jarumta da kuma na barkwanci. An haife shi a ranar 8 ga watan Disambar 1935, kusan shekara 83 ke nan. Sunansa na ainihi Dharam Singh Deol, an kuma an haife shi a kauyen Nasrali da ke gundumar Ludhiana a yankin Punjab. Dharmendra bai yi karatu mai zurfi ba, kuma an masa aure da wuri, domin tun yana da shekara 19 a duniya iyayensa suka aura masa Parkash Kaur a shekarar 1954. sun haifi 'ya'ya biyu maza, wato Sunny Deol da Bobby Deol. Yaushe ya fara fitowa a fim Dharmendra ya fara fim ne tun zamanin fina-finai marasa launi, ma'ana tun zamanin hoton bidiyo fari da baki. Ya fara fim ne a shekarar 1960, in da ya fito a matsayin mataimakin jarumi, wato supporting actor a fim din Dil Bhi Tera Hum Bhi Tere. Daga nan ne kuma ya ci gaba da fitowa a fina-finai. Sai dai kuma fina-finansa na shekarun 1970, sun fi haskaka shi d