Yadda mata ke karuwanci don burge mutane a Kenya





Mata matasa na amfani da maza 'yan daduro wajen samun kudaden da za su yi rayuwa don burge mutane a kafafan sada zumunta a kasar Kenya.
Wata mai shirya fina-finai, Nyasha Kadandara, ta ce mata na amfani da karuwanci wajen kawar da talauci, amma kuma a yanzu ya zamo abin burgewa.
BBC ta gudanar da bincike a kan wasu mata uku.
Ta farko mai buge-buge ce, sunanta Kal, mace ce mai da amma kuma ba ta da miji kuma tana rawa a gidajen rawa musamman da daddare, sannan babban burinta shi ne ta zamo tauraruwa.
Ta je Kenya in da ta nemi mai kudin da zai dauki nauyinta wato daduron da zai cika mata burinta ta zama mawakiya.
Me ya sa matan Najeriya marsa auren ke wahalar samun gida?
'Za a iya koma wa gidan jiya game da annobar cutar HIV'
Jamus: Za a rika biyan nakasassu kudin lalata da karuwai
To amma kuna ganin wannan hanya ce mai sauki da mutum zai samu kudi?
Mace ta biyu daliba ce.
Yawanci dalibai a birnin Nairobi sun fi son yin soyayya da tsofaffi maza maimakon daidai su.
Jane 'yar shekara 21 ce kuma daliba ce, koda yake ta fito ne daga wani kauye wadanda suke daraja al'ada.
Ta ce ta na samu taimakon karatunta ne daga wajen wasu daduronta tsofaffi guda biyu.
Mace ta uku Bridget Achieng, mai tallan kayan kawa ce kuma ta shahara a wasu shirye-shirye da ake nuna wa a gidan talabijin.
Ta ce ta samu wannan rayuwa ne ta hanyar kwanciya da manyan masu hannu da shuni.

Comments

Popular posts from this blog

Dadin kowa sabon salo episode 15

Dadin kowa sabon salo episode 15