A makon da ya gabata mun tsaya wajen da SHEIKH ABDULJABBAR NASIRU KABARA ya ke bayani kan sahabbai, inda ya ce sahabbai kashi biyu ne; akwai Mukhlisai akwai Munafukai. Don haka za mu cigaba da tattaunawa da ya yi tare da wakilin LEADERSHIP A YAU LAHADI, RABIU ALI INDABAWA , kamar haka: Sahabbai iri biyu ne; akwai Mukhlisai muminai na Allah, wadannan su ne sahabbai na kirki, akwai munafukai. To, ni yakin da a ke da ni shi ne, cewa da a ke munafukan nan da Mukhlisan nan duk daya ne, sai na ke ga ba a yi wa Allah adailci ba, ba a yi wa manzon Allah ba, ba a yi ma sa biyayya ba. Kuma maganar nan ba ni kadai na yi ta ba. Malamai da yawa sun yi ta, iya abinda na fada ma rigimar nan da ta shiga ta mulki a cikin abin masu mulki a hannu su su ka aikata zaluncin nan, su ka binne al’amuran, su ka sayi malamai, sai abu ya taho a haka, wanda ya yi bincike zai gane gaskiyar abin kamar yadda ta ke faruwa yanzu. To, wannan gaskiyar idan ka fito da ita sai a ce ka zagi sahabbai. Na ba ka misalin wani